Zabura 130 - Littafi Mai TsarkiSa Zuciya ga Ceton Allah 1 A cikin fid da zuciyata, Na yi kira gare ka, ya Ubangiji. 2 Ka ji kukana, ya Ubangiji, Ka kasa kunne ga kiran da nake yi na neman taimako! 3 Idan kana yin lissafin zunubanmu, Wa zai kuɓuta daga hukunci? 4 Amma kakan gafarta mana, Domin mu zama masu tsoronka. 5 Na zaƙu, ina jiran taimako daga Ubangiji, Ga maganarsa na dogara. 6 Ina jiran Ubangiji, Na zaƙu ƙwarai, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir, I, fiye da matsara waɗanda suke jiran ketowar alfijir. 7 Ya Isra'ila, ki dogara ga Ubangiji, Saboda ƙaunarsa madawwamiya ce, A koyaushe yana da nufin yin gafara. 8 Zai fanshi jama'arsa Isra'ila Daga dukan zunubansu. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria