Zabura 128 - Littafi Mai TsarkiAlbarkar Mai Tsoron Ubangiji 1 Mai farin ciki ne wanda yake tsoron Ubangiji, Wanda yake zamansa bisa ga umarnansa! 2 Za ka sami isasshen abin biyan bukatarka, Za ka yi farin ciki ka arzuta. 3 Matarka za ta zama kamar kurangar inabi Mai 'ya'ya a gidanka, 'Ya'yanka maza kuma kamar dashen zaitun Suna kewaye da teburinka. 4 Mutumin da yake yi wa Ubangiji biyayya, Hakika za a sa masa albarka kamar haka. 5 Ubangiji ya sa maka albarka daga Sihiyona! Ya sa ka ga Urushalima ta arzuta Dukan kwanakinka! 6 Ya kuma sa ka ka ga jikokinka! Salama ta kasance ga Isra'ila! |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria