Zabura 12 - Littafi Mai TsarkiAddu'ar Neman Taimako 1 Ka cece ni, ya Ubangiji, Ba sauran mutanen kirki, Ba kuma za a sami amintattun mutane ba. 2 Dukan mutane suna yi wa juna ƙarya, Suna ruɗin junansu da yaudara. 3 Ka sa harsunan nan masu yaudara su yi shiru, Ya Ubangiji, ka rufe bakunan nan masu fāriya! 4 Sukan ce, “Za mu yi magana yadda muka ga dama, Ba kuwa wanda zai hana mu. Wane ne yake da ikon faɗa mana abin da za mu faɗa?” 5 Ubangiji ya ce, “Amma zan zo yanzu, Domin ana zaluntar masu bukata, Waɗanda aka tsananta musu kuma, suna nishi don zafi. Zan ba su zaman lafiya da suke nema!” 6 Alkawaran Ubangiji abin dogara ne, Alkawarai ne na ainihi kamar azurfa Da aka tace har sau bakwai cikin matoya. 7 Ka kiyaye lafiyarmu, ya Ubangiji, Ka kiyaye mu daga irin waɗannan mutane. 8 Akwai mugaye ko'ina, suna ta yanga, Suna ta yabon abin da yake mugunta. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria