Zabura 114 - Littafi Mai TsarkiWaƙar Idin Ƙetarewa 1 Sa'ad da jama'ar Isra'ila suka bar Masar, Sa'ad da zuriyar Yakubu suka bar baƙuwar ƙasar nan, 2 Yahuza ya zama tsattsarkar jama'ar Ubangiji, Isra'ila ya zama abin mallakarsa. 3 Bahar Maliya da ya duba, sai ya gudu, Kogin Urdun ya daina gudu. 4 Duwatsu suka yi ta tsalle kamar awaki, Tuddai kuwa suka yi ta tsalle suna kewayawa kamar tumaki. 5 Me ya faru ne, ya teku, da ya sa ki gudu? Kai fa Urdun, me ya sa ka daina gudu? 6 Ku fa duwatsu, me ya sa kuka yi ta tsalle kamar awaki? Tuddai, me ya sa kuka yi ta tsalle, Kuna kewayawa kamar tumaki? 7 Ki yi rawar jiki, ya ke duniya, Saboda zuwan Ubangiji, A gaban Allah na Yakubu, 8 Wanda ya sa duwatsu su zama tafkunan ruwa, Ya kuma sa kogwannin duwatsu su zama maɓuɓɓugai, Masu bulbulo da ruwa. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria