Zabura 110 - Littafi Mai TsarkiUbangiji Ya Ba Sarkin da Ya Zaɓa Iko 1 Ubangiji ya ce wa Mai Girma, Sarkina, “Zauna nan a damana, Har in sa maƙiyanka a ƙarƙashin sawayenka.” 2 Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce, “Ka yi mulki bisa maƙiyanka.” 3 A ranar da za ka yi yaƙi da maƙiyanka, Jama'arka za su kawo maka gudunmawa don kansu. Kamar yadda raɓa take da sassafe, Haka samarinka za su zo wurinka a tsarkakan tsaunuka. 4 Ubangiji ya yi muhimmin alkawari, Ba kuwa zai fasa ba! “Za ka zama firist har abada Bisa ga tsabi'ar Malkisadik firist.” 5 Ubangiji yana damanka, Zai kori sarakuna a ranar da ya husata. 6 Zai shara'anta wa dukan sauran al'umma, Ya rufe fagen fama da gawawwaki, Zai kori sarakunan duk duniya. 7 Sarkin zai sha ruwan rafin da yake kan hanya, Ya wartsake ya sami ƙarfi. Zai yi tsayawar nasara. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria