Zabura 11 - Littafi Mai TsarkiMafakar Adalai 1 Na dogara ga Ubangiji domin zaman lafiya, Wauta ce idan kun ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu, 2 Domin mugaye sun ja bakkunansu, Sun kuma ɗana kibansu Domin su harbi mutanen kirki a duhu. 3 Ba abin da mutumin kirki zai iya yi Sa'ad da kome ya lalace.” 4 Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa, Yana da kursiyinsa a Sama. Yana kallon dukan mutane Yana sane da abin da suke yi. 5 Yana auna masu kirki da mugaye dukka, Yana ƙin marar bin doka gaba ɗaya. 6 Yakan aukar da garwashin wuta Da kibritu mai cin wuta a kan mugaye, Yakan hukunta su da harshen wuta mai ƙuna. 7 Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar kyawawan ayyuka, Masu yi masa biyayya za su zauna a gabansa. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria