Zabura 101 - Littafi Mai TsarkiAlkawarin Sarki domin Zaman Adalci 1 Waƙata ta aminci ce da gaskiya. Ina raira maka ita, ya Ubangiji. 2 Abin da nake yi ba zai zama laifi ba, Yaushe za ka zo wurina? Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana. 3 Ba zan jure da mugunta ba ko kaɗan. Na ƙi jinin ayyukan waɗanda suka bijire wa Allah, Ba ruwana da su. 4 Ba zan yi rashin aminci ba, Ba kuwa zan yi tunanin mugunta ba. 5 Zan hallakar da mai raɗar abokinsa, Ba zan jure da mutum mai girmankai, Ko mai alfarma ba. 6 Zan yarda da waɗanda suke amincewa da Allah, Zan yardar musu si yi zamansu a fādata, Zan yarda wa waɗanda suke da tabbataccen aminci Su yi mini hidima. 7 Maƙaryaci ba zai zauna a fādata ba, Ba zan yarda munafuki ya yi zamansa a wurina ba. 8 A kowace rana zan yi ta karkashe dukan mugayen da suke cikin ƙasarmu, Zan kori dukan mugaye daga birnin Ubangiji. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria