Zabura 1 - Littafi Mai TsarkiLITTAFI NA FARI ( Zab 1—41 ) Farin Ciki na Gaskiya 1 Albarka ta tabbata ga mutumin da Ba ya karɓar shawarar mugaye, Wanda ba ya bin al'amuran masu zunubi, Ko ya haɗa kai da masu wasa da Allah. 2 Maimakon haka, yana jin daɗin karanta shari'ar Allah, Yana ta nazarinta dare da rana. 3 Yana kama da itacen da yake a gefen ƙorama, Yakan ba da 'ya'ya a kan kari, Ganyayensa ba sa yin yaushi, Yakan yi nasara a dukan abin da yake yi. 4 Amma mugaye ba haka suke ba, Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa. 5 Allah kuwa zai hukunta mugaye, Masu zunubi kuwa za a ware su daga adalai. 6 Gama Ubangiji yana lura da al'amuran adalai, Amma al'amuran mugaye za su watse. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria