Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Yowel 3 - Littafi Mai Tsarki


Shari'ar Al'ummai

1 “A wannan lokaci zan mayar wa Yahuza da Urushalima da wadatarsu.

2 Zan tattara dukan al'ummai, In kai su kwarin Yehoshafat. A can zan yi musu shari'a A kan dukan abin da suka yi wa jama'ata. Sun warwatsa Isra'ilawa a sauran ƙasashe, Suka rarraba ƙasata.

3 Sun jefa kuri'a a kan mutanena, Sun sayar da yara, mata da maza, zuwa bauta Don su biya karuwai da ruwan inabi.

4 “Taya da Sidon, da dukan Filistiya, me kuke so ku yi mini? Kuna ƙoƙari ku rama mini saboda wani abu? Idan haka ne, zan rama muku da gaggawa.

5 Kun kwashe azurfata da zinariyata kun kuma washe taskata, kun kai cikin haikalinku.

6 Kun kwashe mutanen Yahuza da Urushalima, kun kai su nesa da ƙasarsu, sa'an nan kun sayar da su ga Helenawa.

7 Yanzu zan dawo da su daga wuraren da kuka sayar da su, zan yi muku abin da kuka yi musu.

8 Zan sa a sayar wa mutanen Yahuza 'ya'yanku mata da maza, su kuma za su sayar da su ga Sabiyawa, can nesa. Ni Ubangiji na faɗa.”

9 Ku sanar wa al'ummai da wannan, Su yi shirin yaƙi, Su kira mayaƙa! Su tattaro sojoji, su zo!

10 Su bubbuge allunan garmunansu, Su yi takuba da su. Su ƙera māsu da wuƙaƙen da ake yi wa itatuwa aski. Sai marar ƙarfi ya ce, “Ni jarumi ne!”

11 Su gaggauta, su zo su al'ummai da suke kewaye, Su tattaru a kwarin. “Ya Ubangiji, ka saukar da rundunarka mai ƙarfi.”

12 “Sai al'ummai su yi shiri, Su zo kwarin Yehoshafat, Gama a can zan zauna in shara'anta al'umman da suke kewaye,

13 Su sa lauje gama hatsin ya isa girbi. Su shiga su tattaka, Gama wurin matsewar ruwan inabi ya cika. Manyan randuna sun cika suna tumbatsa, Gama muguntarsu da yawa take.”

14 Dubun dubbai suna cikin kwarin da za a yanke shari'a! Gama ranar Ubangiji ta kusa zuwa a kwarin yanke shari'a.

15 Rana da wata sun yi duhu, Taurari kuma ba su haskakawa.


Ceton Yahuza

16 Ubangiji yana magana da ƙarfi daga Sihiyona, Yana tsawa daga Urushalima, Sammai da duniya sun girgiza. Amma Ubangiji shi ne mafakar jama'arsa, Shi ne kagarar mutanen Isra'ila.

17 “Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake zaune a Sihiyona, tuduna tsattsarka. Urushalima kuma za ta tsarkaka, Sojojin abokan gāba ba za su ƙara ratsawa ta cikinta ba.

18 “A wannan lokaci tsaunuka za su rufu da kurangar inabi, Tuddai za su cika da shanu, Dukan rafuffukan Yahuza za su gudano da ruwa, Maɓuɓɓuga za ta gudano daga Haikalin Ubangiji, Ta shayar da kwarin Shittim.

19 “Masar za ta zama hamada, Edom kuma za ta zama kufai, Saboda kama-karya da suka yi wa mutanen Yahuza, Saboda sun zubar da jinin marasa laifi a ƙasarsu,

20 Za a zauna a Yahuza da Urushalima dukan tsararraki har abada.

21 Zan sāka alhakin jininsu, Ba zan kuɓutar da mai laifi ba, Gama Ubangiji yana zaune a Sihiyona.”

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan