Yowel 2 - Littafi Mai TsarkiFāra ta Zama Musu Alamar Ranar Ubangiji 1 Ku busa ƙaho, ku yi gangami, A cikin Sihiyona, tsattsarkan dutsen Allah! Duk mutanen ƙasar za su yi rawar jiki, Domin ranar Ubangiji tana zuwa, ta yi kusa. 2 Za ta zama rana ce mai duhu dulum, Ranar gizagizai ce baƙi ƙirin. Runduna mai ƙarfi tana tasowa, Kamar ketowar hasken safiya bisa tsaunuka. Faufau ba a taɓa ganin irinta ba, Ba kuwa za a sāke ganin irinta ba. 3 Tana cinye shuke-shuke kamar wuta, Ƙasa kamar gonar Adnin take kafin ta zo, Amma a bayanta ta zama hamada, Ba abin da ya tsere mata. 4 Kamar doki take, Tana gudu kamar dokin yaƙi. 5 Motsin tsallenta a kan duwatsu kamar Motsin karusa ne. Kamar kuma amon wutar da take cin tattaka. Kamar runduna mai ƙarfi wadda ta ja dāgar yaƙi. 6 Da zuwanta mutane sukan firgita, Dukan fuskoki sukan ɓaci. 7 Takan auka kamar mayaƙa, Takan hau garu kamar sojoji, Takan yi tafiya, Kowa ta miƙe sosai inda ta sa gaba, Ba ta kaucewa. 8 Ba ta hawan hanyar juna, Kowa tana bin hanyarta. Takan kutsa cikin abokan gāba, ba a iya tsai da ita. 9 Takan ruga cikin birni, Takan hau garu a guje, Takan hau gidaje, Takan shiga ta tagogi kamar ɓarawo. 10 Duniya takan girgiza saboda ita, Sammai sukan yi rawar jiki. Rana da wata sukan duhunta, Taurari kuwa sukan daina haskakawa. 11 Ubangiji yakan umarci rundunarsa, Rundunarsa mai cika umarninsa babba ce, mai ƙarfi, Gama ranar Ubangiji babba ce mai banrazana. Wa zai iya daurewa da ita? Jinƙan Ubangiji 12 “Koyanzu,” in ji Ubangiji, “Ku juyo wurina da zuciya ɗaya, Da azumi, da kuka, da makoki, 13 Ku kyakkece zuciyarku, ba tufafinku kaɗai ba.” Ku komo wurin Ubangiji Allahnku. Gama shi mai alheri ne, mai jinƙai, Mai jinkirin fushi ne, mai yawan ƙauna, Yakan tsai da hukunci. 14 Wa ya sani ko Ubangiji Allahnmu zai sāke nufinsa, Ya sa mana albarka, Har mu miƙa masa hadaya ta gari da ta sha? 15 Ku busa ƙaho a Sihiyona, Ku sa a yi azumi, Ku kira muhimmin taro. 16 Ku tattara jama'a wuri ɗaya, Ku tsarkake taron jama'a, Ku tattara dattawa da yara, Har da jarirai masu shan mama. Ku sa ango ya fito daga cikin turakarsa, Amarya kuma ta fito daga cikin ɗakinta. 17 Sai firistoci masu hidimar Ubangiji, Su yi kuka a tsakanin shirayi da bagade, Su ce, “Ya Ubangiji, ka ceci jama'arka, Kada ka bar gādonka ya zama abin zargi Da abin ba'a a tsakiyar al'ummai. Don kada al'ummai su ce, ‘Ina Allahnsu?’ ” 18 Sai Ubangiji ya ji kishin ƙasarsa, Ya kuma ji ƙan mutanensa. 19 Sa'an nan ya ce musu, “Ga shi, zan ba ku hatsi da ruwan inabi, da mai, Za ku ƙoshi. Ba zan sa ku ƙara zama abin zargi ga al'ummai ba. 20 Zan kawar muku da waɗanda suka zo daga arewa, Zan kori waɗansunsu zuwa cikin hamada. Zan kori sahunsu na gaba zuwa cikin Tekun Gishiri, Zan kori sahunsu na baya, zuwa cikin Bahar Rum. Gawawwakinsu za su yi ɗoyi. Zan yi musu haka saboda dukan abin da suka yi muku.” 21 Kada ki ji tsoro, ya ƙasa, Ki yi farin ciki, ki yi murna, Gama Ubangiji ne ya yi waɗannan manyan al'amura. 22 Kada ku ji tsoro, ku dabbobin saura, Gama wuraren kiwo a jeji sun yi kore shar. Itatuwa suna ta yin 'ya'ya, Itacen ɓaure da kurangar inabi suna ta yin 'ya'ya sosai. 23 Ya ku mutanen Sihiyona, ku yi murna, Ku yi farin ciki da Ubangiji Allahnku, Gama ya ba ku ruwan farko Domin shaidar gafarar da ya yi muku, Ya kwararo muku da ruwan farko da na ƙarshe da yawa kamar dā. 24 Masussukai za su cika da hatsi, Wuraren matse ruwan inabi za su malala da ruwan inabi. 25 “Zan mayar muku da abin da kuka yi hasararsa A shekarun da fara ta cinye amfaninku, Wato ɗango da fara mai gaigayewa, da mai cinyewa, Su ne babbar rundunata wadda na aiko muku. 26 Yanzu za ku ci abinci a wadace ku ƙoshi, Za ku yabi sunan Ubangiji Allahnku, Wanda ya yi muku abubuwa masu banmamaki, Ba kuma za a ƙara kunyatar da mutanena ba. 27 Ku mutanen Isra'ila, za ku sani ina cikinku, Ni ne kuwa Ubangiji Allahnku, ba wani kuma, Ba kuma za a ƙara kunyatar da mutanena ba.” Za a Ba da Ruhun Allah 28 “Bayan wannan zan zubo Ruhuna a kan jama'a duka, 'Ya'yanku mata da maza za su iyar da saƙona, Tsofaffinku kuwa za su yi mafarkai, Samarinku za su ga wahayi da yawa. 29 A lokacin zan zubo Ruhuna, Har a kan barori mata da maza. 30 “Zan yi faɗakarwa a kan wannan rana A sararin sama da a duniya. Za a ga jini, da wuta, da murtukewar hayaƙi, 31 Rana za ta duhunta, Wata zai zama ja wur kamar jini, Kafin isowar babbar ranan nan mai bantsoro ta Ubangiji. 32 Amma dukan waɗanda suka nemi Ubangiji za su tsira. Kamar yadda Ubangiji ya ce, Akwai waɗanda suke a Dutsen Sihiyona da Urushalima Da za su tsira, Waɗannan da Ubangiji ya zaɓa za su tsira.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria