Nehemiya 7 - Littafi Mai TsarkiNehemiya Ya Zaɓi Masarautan Urushalima 1 Sa'ad da aka gina garun, aka sa ƙofofinsa, aka kuma sa matsaran ƙofofi, da mawaƙa, da Lawiyawa, 2 sai na ba ɗan'uwana, Hanani, da Hananiya, shugaban kagara, aikin riƙon Urushalima. Shi Hananiya mai aminci ne, mai tsoron Allah, fiye da sauran mutane. 3 Sa'an nan na ce musu, kada su buɗe ƙofofin Urushalima da sassafe, sai rana ta cira sosai, su kuma kulle ƙofofin da ƙarfe kafin matsara su tashi wajen faɗuwar rana. Su samo matsara daga mazaunan Urushalima, su sa su tsaye a muhimman wurare, waɗansunsu kuma suna zaga gidaje. Lissafin Mutane ( Ezra 2.1-70 ) 4 Birnin yana da faɗi da girma, amma mutanen da suke ciki kaɗan ne, ba a kuma gina gidaje ba tukuna. 5 Allahna kuwa ya sa a zuciyata in tara manya da shugabanni, da sauran jama'a don a rubuta su bisa ga asalinsu. Na sami littafin asali na waɗanda suka fara komowa. Ga abin da na tarar aka rubuta ciki. 6 Waɗannan su ne mutanen lardin Yahuza, waɗanda suka komo daga zaman talala da Nebukadnezzar Sarkin Babila ya kai mutane. Sun komo Urushalima da Yahuza. Kowa ya tafi garinsu. 7 Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seraiya, da Re'elaya, da Nahamani, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba'ana. 8-25 Ga jerin iyalan Isra'ila da adadin waɗanda suka komo daga zaman dole iyalin Farosh, dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172) iyalin Shefatiya, ɗari uku da saba'in da biyu iyalin Ara, ɗari shida da hamsin da biyu iyalin Fahat-mowab, wato zuriyar Yeshuwa da Yowab, dubu biyu da ɗari takwas da goma sha takwas (2,818) iyalin Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) iyalin Zattu, ɗari takwas da arba'in da biyar iyalin Zakkai, ɗari bakwai da sittin iyalin Bani, ɗari shida da arba'in da takwas iyalin Bebai, ɗari shida da ashirin da takwas iyalin Azgad, dubu biyu da ɗari uku da ashirin da biyu (2,322) iyalin Adonikam, ɗari shida da sittin da bakwai iyalin Bigwai, dubu biyu da sittin da bakwai (2,067) iyalin Adin, ɗari shida da hamsin da biyar iyalin Ater (na Hezekiya), tasa'in da takwas iyalin Hashum, ɗari uku da ashirin da takwas iyalin Bezai, ɗari uku da ashirin da huɗu iyalin Yora, ɗari da goma sha biyu iyalin Gibeyon, tasa'in da biyar. 26-38 Mutanen da kakanninsu suka zauna a waɗannan garuruwa, su ma sun komo daga zaman talala. Baitalami da Netofa, ɗari da tamanin da takwas Anatot, ɗari da ashirin da takwas Azmawet, arba'in da biyu Kiriyat-yeyarim da Kefira, da Biyerot, ɗari bakwai da arba'in da uku Rama da Geba, ɗari shida da ashirin da ɗaya Mikmash, ɗari da ashirin da biyu Betel da Ai, ɗari da ashirin da uku Da wani Nebo, hamsin da biyu Da wani Elam, dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) Harim, ɗari uku da ashirin Yariko, ɗari uku da arba'in da biyar Lod, da Hadid, da Ono, ɗari bakwai da ashirin da ɗaya Senaya, dubu uku da ɗari tara da talatin (3,930). 39-42 Ga lissafin iyalin firistoci da suka komo daga zaman talala. Yedaiya, na zuriyar Yeshuwa, ɗari tara da saba'in da uku Immer, dubu ɗaya da hamsin da biyu (1,052) Fashur, dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247) Harim, dubu ɗaya da goma sha bakwai (1,017). 43 Lawiyawan da suka komo daga zaman talala, Yeshuwa da Kadmiyel na zuriyar Hodawiya, saba'in da huɗu. 44 Mawaƙa, na zuriyar Asaf, ɗari da arba'in da takwas. 45 Masu tsaron Haikali su ne zuriyar Shallum, da Ater, da Talmon, da Akkub, da Hatita, da Shobai, ɗari da talatin da takwas. 46-56 Ma'aikatan Haikali da suka komo daga zaman talala, su ne Zuriyar Ziha, da Hasufa, da Tabbawot, Keros, da Siyaha, da Fadon, Lebana, da Hagaba, da Shamlai, Hanan, da Giddel, da Gahar, Rewaiya, da Rezin, da Nekoda, Gazam, da Uzza, da Faseya, Besai, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa, Bakbuk, da Hakufa, da Harkur, Bazlut, da Mehida, da Harsha, Barkos, da Sisera, da Tema, Neziya, da Hatifa. 57-59 Iyalan barorin Sulemanu da suka komo daga zaman talala, su ne na Sotai, da Hassoferet, da Feruda, Yawala, da Darkon, da Giddel, Shefatiya, da Hattil, da Fokeret-hazzebayim, da Ami. 60 Jimillar zuriyar ma'aikatan Haikali da na Sulemanu, su ɗari uku da tasa'in da biyu ne. 61-62 Waɗannan su ne daga zuriyar Delaiya, da Tobiya, da Nekoda, waɗanda suka zo daga garuruwan Telmela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya nuna gidajen kakanninsu, ko zuriyarsu a cikin Isra'ilawa ba, su ɗari shida ne da arba'in da biyu. 63 Na wajen firistoci kuma su ne zuriyar Habaya, da na Hakkoz, da na Barzillai, wanda ya auri 'yar Barzillai mutumin Gileyad, aka kira shi da sunan zuriyar surukinsa. 64 Waɗannan suka nema a rubuta su tare da waɗanda aka rubuta jerin sunayen asalinsu, amma ba a same su a ciki ba, saboda haka aka hana su shiga cikin firistoci, sun zama kamar marasa tsarki. 65 Sai mai mulki ya faɗa musu kada su ci abinci mafi tsarki, sai an sami firist wanda zai yi tambaya ta wurin Urim da Tummin tukuna. 66-69 Jimillar waɗanda suka komo duka su dubu arba'in da dubu biyu da ɗari uku da sittin ne (42,360) barorinsu mata da maza, waɗanda yawansu ya kai dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337) mawaƙa ɗari biyu da arba'in da biyar mata da maza dawakansu kuma ɗari bakwai da talatin da shida ne alfadaransu kuma ɗari biyu da arba'in da biyar ne raƙumansu ɗari huɗu da talatin da biyar ne jakunansu dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720) 70-72 Da yawa daga cikin jama'a suka ba da taimako domin biyan aikin gyaran Haikali. Mai mulki ya ba da zinariya darik dubu (1,000) kwanonin wanke hannu guda hamsin rigunan firistoci ɗari biyar da talatin Shugabannin iyali suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu da ɗari biyu (2,200) Sauran jama'a suka ba da zinariya darik dubu ashirin (20,000) azurfa maina dubu biyu (2,000) rigunan firistoci guda sittin da bakwai. 73 Sa'an nan firistoci, da Lawiyawa, da masu tsaron Haikali, da mawaƙa da waɗansu da dama daga cikin jama'a, da ma'aikatan Haikali, da dukan Isra'ilawa suka zauna a garuruwansu. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria