Nehemiya 12 - Littafi Mai TsarkiFiristoci da Lawiyawa 1 Firistoci da Lawiyawa da suka komo tare da Zarubabel ɗan Sheyaltiyel, da Yeshuwa, su ne Seraiya, da Irmiya, da Ezra, 2-7 Amariya, da Malluki, da Hattush, Shekaniya, da Rehum, da Meremot, Iddo, da Ginneton, da Abaija, Miyamin, da Mawadiya, da Bilga, Shemaiya, da Yoyarib, da Yedaiya, Sallai, da Amok, da Halkiya, da Yedaiya. Waɗannan su ne shugabannin firistoci da 'yan'uwansu a zamanin Yeshuwa. 8-9 Lawiyawa su ne, Yeshuwa, da Binnuyi, da Kadmiyel, Sherebiya, da Yahuza, da Mattaniya wanda yake lura da waƙoƙin godiya, da shi da 'yan'uwansa. Bukbukiya da Unno, 'yan'uwansu, suka tsaya daura da su a taron sujada. Zuriyar Yeshuwa Firist 10 Yeshuwa shi ne ya haifi Yoyakim, Yoyakim ya haifi Eliyashib, Eliyashib ya haifi Yoyada. 11 Yoyada ya haifi Jonatan, Jonatan ya haifi Yadduwa. Shugabannin Iyalin Firistoci 12-21 A zamanin Yoyakim babban firist, waɗannan su ne shugabannin iyalin firistoci, na wajen Seraiya, Meraiya ne na wajen Irmiya, Hananiya ne na wajen Ezra, Meshullam ne na wajen Amariya, Yehohanan ne na wajen Malluki, Jonatan ne na wajen Shebaniya, Yusufu ne na wajen Harim, Adana ne na wajen Merayot, Helkai ne na wajen Iddo, Zakariya ne na wajen Ginneton, Meshullam ne na wajen Abaija, Zikri ne na wajen Miniyamin da Mowadiya, Filtai ne na wajen Bilga, Shimeya ne na wajen Shemaiya, Yehonatan ne na wajen Yoyarib, Mattenai ne na wajen Yedaiya, Uzzi ne na wajen Sallai, Kallai ne na wajen Amok, Eber ne na wajen Hilkiya, Hashabiya ne na wajen Yedaiya, Netanel ne. Lissafin Manya na Iyalin Firistoci da Lawiyawa 22 A zamanin Eliyashib, da Yoyada, da Yohenan, da Yadduwa, Lawiyawa, har zuwa zamanin mulkin Dariyus, mutumin Farisa, aka rubuta shugabannin gidajen kakannin Lawiyawa da firistoci. 23 Aka kuma rubuta shugabannin gidajen kakannin zuriyar Lawi a tarihi, har zuwa zamanin Yohenan ɗan Eliyashib. An Rarraba Ayyukan Haikali 24 Shugabannin Lawiyawa kuwa, su ne Hashabiya, da Sherebiya, da Yeshuwa, da Kadmiyel. 'Yan'uwansu suna tsaye kusa da su daki daki domin su yi yabo, su yi godiya kamar yadda Dawuda mutumin Allah ya umarta. 25 Mattaniya, da Bakbukiya, da Obadiya, da Meshullam, da Talmon, da Akkub su ne masu tsaron ƙofofi, suna tsaron ɗakunan ajiya na wajen ƙofofi. 26 Waɗannan suna nan a zamanin Yoyakim ɗan Yeshuwa, jikan Yehozadak, da zamanin mai mulki Nehemiya, da Ezra, firist da magatakarda. An Keɓe Garun Birni 27 A lokacin keɓe garun Urushalima, sai aka nemo Lawiyawa a wurarensu duka don a kawo su Urushalima, su yi bikin keɓewa da farin ciki da godiya, da raira waƙoƙi da kuge, da garaya, da molo. 28 Aka tattara mawaƙa daga kewayen Urushalima da ƙauyukan Netofatiyawa. 29 Da kuma daga Betgilgal da karkarar Geba, da Azmawet, gama mawaƙan sun gina wa kansu ƙauyuka kewaye da Urushalima. 30 Sai firistoci da Lawiyawa suka tsarkake kansu, suka kuma tsarkake jama'a, da ƙofofi, da garun. 31 Sai na sa shugabannin Yahuza su hawo garu, sa'an nan na sa manyan ƙungiyoyi biyu waɗanda za su yi godiya, su tafi a jere. Ƙungiya guda ta bi wajen dama a kan garun zuwa Ƙofar Juji. 32 Hoshaiya da rabin sugabannin Yahuza suka bi bayansu, 33 tare da Azariya, da Ezra, da Meshullam, 34 da Yahuza, da Biliyaminu, da Shemaiya, da Irmiya. 35 Sa'an nan waɗansu 'ya'yan firistoci, masu busar ƙaho, su ne Zakariya ɗan Jonatan, jīkan Shemaiya. Sauran kakanninsa su ne Mattaniya, da Mikaiya, da Zakkur, daga zuriyar Asaf. 36 Sauran 'yan'uwansa su ne Shemaiya, da Azarel, da Milalai, da Gilalai, da Ma'ai, da Netanel, da Yahuza, da Hanani. Suna da kayayyakin bushe-bushe da na kaɗekaɗe. Ezra magatakarda ne yake gabansu. 37 A Ƙofar Maɓuɓɓuga kuwa, sai suka yi gaba sosai wajen matakan birnin Dawuda, wajen hawan garu, daga bisa gidan Dawuda, zuwa Ƙofar Ruwa wajen gabas. 38 Ƙungiyar jama'a ta biyu ta masu yin waƙoƙin godiya, ta bi ta wajen hagu. Na bi su tare da rabin jama'a a kan garu, sama da Hasumiyar Tanderu zuwa garu mai fādi, 39 da Kuma sama da Ƙofar, Ifraimu da wajen Tsohuwar Ƙofar, da wajen Ƙofar Kifi, da Hasumiyar Hananel, da Hasumiyar Ɗari zuwa Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a Ƙofar Tsaro. 40 Haka fa ƙungiyoyi biyu ɗin nan masu raira waƙoƙin godiya suka tsaya a Haikalin Allah. Ni da rabin shugabanni muna tare da su. 41 Tare da firistoci kuma, wato su Eliyakim, da Ma'aseya, da Miniyamin, da Mikaiya, da Eliyehoyenai, da Zakariya, da Hananiya, suna busa ƙaho, 42 da kuma Ma'aseya, da Shemaiya, da Ele'azara, da Uzzi, da Yehohanan, da Malkiya, da Elam, da Ezer, suna raira waƙoƙi, Yezrahiya kuma shi ne shugabansu. 43 Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa. Shiri don Firistoci da Lawiyawa 44 A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi. 45 Sun yi wa Allahnsu sujada, sun yi hidimar tsarkakewa tare da mawaƙa da masu tsaron ƙofofi kamar yadda Dawuda da ɗansa Sulemanu suka umarta. 46 A dā a zamanin Dawuda da Asaf akwai shugaban mawaƙa, akwai kuma waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah. 47 A zamanin Zarubabel da zamanin Nehemiya dukan jama'ar Isra'ila suka biya wa mawaƙa da masu tsaron ƙofofi bukatarsu ta kowace rana. Sun kuma ba Lawiyawa sadokoki, su Lawiyawa kuma suka ba zuriyar Haruna nasu rabo. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria