Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Nahum 3 - Littafi Mai Tsarki

1 Kaiton birnin jini, Wanda yake cike da ƙarairayi da ganima, Da waso kuma ba iyaka!

2 Ku ji amon bulala da kwaramniyar ƙafafu, Da sukuwar doki da girgizar karusai!

3 Sojojin dawakai suna kai sura, Takuba suna walƙiya, māsu suna ƙyalƙyali. Ga ɗumbun kisassu, da tsibin gawawwaki, Matattu ba su ƙidayuwa, Suna tuntuɓe a kan gawawwaki!

4 Ya faru saboda yawan karuwancin Nineba kyakkyawa mai daɗin baki, Wadda ta ɓad da al'umman duniya da karuwancinta, Ta kuma ɓad da mutane da daɗin bakinta.

5 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ina gāba da ke, Zan kware fatarinki a idonki, Zan sa al'ummai da mulkoki su dubi tsiraicinki.

6 Zan watsa miki ƙazanta, In yi miki wulakanci, In maishe ki abin raini.

7 Dukan waɗanda za su dube ki Za su ja da baya su ce, ‘Nineba ta lalace, wa zai yi kuka dominta?’ A ina zan samo miki waɗanda za su ta'azantar da ke?”

8 Kin fi No ne? Wadda take a bakin Nilu, Wadda ruwa ya kewaye ta? Teku ce kagararta. Ruwa ne kuma garunta.

9 Habasha da Masar su ne ƙarfinta marar iyaka, Fut da Libiya su ne kuma mataimakanta.

10 Duk da haka an tafi da ita, an kai ta cikin bauta. An fyaɗa ƙanananta a ƙasa, An yi kacakaca da su a kowace mararraba. An jefa kuri'a a kan manyan mutanenta, Aka ɗaure dukan manyan mutanenta da sarƙoƙi.

11 Ke Nineba kuma za ki bugu, Za a ɓoye ki. Za ki nemi mafaka a wurin maƙiyinki.

12 Dukan kagaranki suna kama da itatuwan ɓaure, Waɗanda 'ya'yansu suka harba. Da an girgiza sai su faɗo a bakin mai sha.

13 Sojojinki kamar mata suke a tsakiyarki! An buɗe wa maƙiyanki ƙofofin ƙasarki. Wuta za ta cinye madogaran ƙofofinki.

14 Ki tanada ruwa domin za a kewaye ki da yaƙi! Ki ƙara ƙarfin kagaranki! Ki tafi kududdufi, ki kwaɓa laka! Ki ɗauki abin yin tubali!

15 A can wuta za ta cinye ki, Takobi zai sare ki, Zai cinye ki kamar fara. Ki riɓaɓɓanya kamar fara. Ki kuma riɓaɓɓanya kamar ɗango.

16 Kin yawaita 'yan kasuwanki suna da yawa fiye da taurari, Amma sun tafi kamar fara waɗanda sukan buɗe fikafikansu su tashi, su tafi.

17 Shugabanninki kamar ɗango suke, Manyan mutanenki kamar cincirindon fāra ne, Suna zaune a kan shinge a kwanakin sanyi, Sa'ad da rana ta fito, sukan tashi su tafi, Ba wanda ya san inda suke.

18 Ya Sarkin Assuriya, masu tsaronka suna barci, Manyan mutanenka suna kwankwance, Mutanenka sun watse cikin duwatsu, Ba wanda zai tattaro su.

19 Ba abin da zai rage zafin rauninka, Rauninka ba ya warkuwa. Duk wanda ya ji labarinka, zai tafa hannuwansa Gama wane ne ba ka musguna wa ba?

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan