Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Nahum 2 - Littafi Mai Tsarki

1 Wanda yake farfashewa ya auko maka, Sai ka sa mutane a kagara, a yi tsaron hanya, Ka yi ɗamara, ka tattaro ƙarfinka duka.

2 Gama Ubangiji zai mayar wa Yakubu da darajarsa kamar ta Isra'ila. Ko da masu washewa sun washe su, Sun kuma lalatar da rassan inabinsu.

3 Garkuwoyin jarumawansa jajaye ne, Sojojinsa kuma suna saye da mulufi. Da ya shirya tafiya, Karusai suna walƙiya kamar harshen wuta, Ana kaɗa mashi da bantsoro.

4 Karusai sun zabura a tituna a haukace. Suna kai da kawowa a dandali, Suna walwal kamar jiniya, Suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.

5 Sai aka kira shugabanni, Suka zo a guje suna tuntuɓe, Suka gaggauta zuwa garu, Suka kafa kagara.

6 An buɗe ƙofofin kogi, Fāda ta rikice.

7 An tsiraita sarauniya, an tafi da ita, 'Yan matanta suna makoki, suna kuka kamar kurciyoyi, Suna bugun ƙirjinsu.

8 Nineba tana kama da tafki wanda ruwansa yake zurarewa, Suna cewa, “Tsaya, tsaya,” Amma ba wanda ya waiga.

9 A washe azurfa! A washe zinariya! Dukiyar ba ta da adadi, Akwai dukiya ta kowane iri.

10 Nineba ta halaka! ta lalace, ta zama kufai! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa! Kwankwaso yana ciwo, Fuskoki duka sun kwantsare!

11 Ina kogon nan na zakoki, Inda aka ciyar da 'ya'yan zaki, Inda zaki da zakanya da kwiyakwiyansu sukan tafi, Su tsere daga fitina?

12 Zaki ya kashe abin da ya ishi kwiyakwiyansa. Ya kaso wa zakanyarsa abin da ya ishe ta. Ya cika kogonsa da ganima.


Ragargajewar Nineba

13 “Ga shi, ina gāba da ke. Ni Ubangiji Allah Mai Runduna na faɗa. Zan ƙone karusanki, Takobi kuwa zai karkashe sagarun zakokinki, Zan hana miki ganima a duniya. Ba za a ƙara jin muryoyin jakadunki ba.”

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan