Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Nahum 1 - Littafi Mai Tsarki


Fushin Ubangiji a kan Nineba

1 Jawabi a kan Nineba ke nan, a littafin wahayin Nahum na Elkosh.

2 Ubangiji Allah mai kishi ne, mai sakayya, Ubangiji mai sakayya ne, mai hasala. Ubangiji yakan ɗauki fansa a kan maƙiyansa. Yana tanada wa maƙiyansa fushi.

3 Ubangiji mai jinkirin fushi ne, Mai Iko Dukka. Ubangiji ba zai kuɓutar da mai laifi ba. Hanyarsa tana cikin guguwa da cikin hadiri, Gizagizai su ne ƙurar ƙafafunsa.

4 Yakan tsauta wa teku, sai teku ta ƙafe. Yakan busar da koguna duka. Bashan da Karmel sukan bushe, Tohon Lebanon yakan yanƙwane.

5 Duwatsu sukan girgiza a gabansa, Tuddai kuma su narke. Duniya ta murtsuke a gabansa, Da dukan mazauna a cikinta.

6 Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa kuma zai iya daurewa da hasalarsa? Yana zuba hasalarsa mai kama da wuta, Duwatsu sukan farfasu a gabansa.

7 Ubangiji mai alheri ne, Shi mafaka ne a ranar wahala. Ya san waɗanda suke fakewa a gare shi.

8 Zai shafe maƙiyansa da ambaliyar ruwa, Zai kuma runtumi maƙiyansa zuwa cikin duhu.

9 Me kuke ƙullawa game da Ubangiji? Ubangiji zai wofintar da abin nan da kuke ƙullawa, Sau ɗaya kawai zai hallaka ku.

10 Suna maye da abin shansu, Za su ƙone kamar sarƙaƙƙiyar ƙaya, Da busasshiyar ciyawa.

11 Daga cikinki wani ya fito, Wanda ya ƙulla wa Ubangiji makirci, Ya ƙulla shawara marar amfani.

12 Ni Ubangiji na ce, “Ko da yake suna da ƙarfi, suna kuma da yawa, Za a datse su, su ƙare. Ko da yake na wahalar da kai, Ba zan ƙara wahalar da kai ba.

13 Yanzu zan karya karkiyarsa daga wuyanka, Zan kuma tsinke sarƙarta.”

14 Ubangiji ya riga ya yi umarni a kanka cewa, “Sunanka ba zai ci gaba ba, Zan farfashe sassaƙaƙƙun siffofi Da siffofi na zubi daga gidan gumakanka. Zan shirya maka kabari, gama kai rainanne ne.”


Labarin Fāɗuwar Nineba

15 Duba a kan duwatsu, ƙafafun wanda yake kawo albishir, Wanda yake shelar salama! Ya Yahuza, ka yi bikin idodinka, Ka kuma cika wa'adodinka. Gama mugun ba zai sāke zuwa ya yi gāba da kai ba, An datse shi ƙaƙaf.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan