Mika 7 - Littafi Mai TsarkiLalacewar Isra'ila 1 Tawa ta ƙare, gama na zama kamar lokacin da aka gama tattara amfanin gona, Kamar lokacin da aka gama kalar 'ya'yan inabi, Ba nonon inabi da za a tsinka, a ci, Ba kuma 'ya'yan ɓaure da suka harba wanda raina yake so. 2 Mutanen kirki sun ƙare a duniya, Ba nagarta a cikin mutane. Dukansu suna kwanto don su zub da jini. Kowa yana farautar ɗan'uwansa da tarko. 3 Sun himmantu su aikata abin da yake mugu da hannuwansu. Sarki da alƙali suna nema a ba su hanci, Babban mutum kuma yana faɗar son zuciyarsa, Da haka sukan karkatar da zance. 4 Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake, Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingen ƙaya yake. Ranar da kuka sa mai tsaro, A ran nan za a aukar muku da hukunci. Yanzu ruɗewarku ta zo, 5 Kada ka dogara ga maƙwabcinka, Kada kuma ka amince da abokinka. Ka kuma kame bakinka daga matarka Wadda take kwance tare da kai. 6 Gama ɗa yana raina mahaifi, 'Ya kuma tana tayar wa mahaifiyarta, Matar ɗa kuma tana gāba da surukarta, Mutanen gidan mutum su ne maƙiyansa. Ubangiji Zai Kawo Haske da Ceto 7 Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji, Zan jira ceton Allahna, Allahna zai ji ni. 8 Ya maƙiyina, kada ka yi murna a kaina, Gama sa'ad da na fāɗi, zan tashi kuma. Sa'ad da na zauna cikin duhu, Ubangiji zai haskaka ni. 9 Zan ɗauka fushin Ubangiji ne, Gama na yi masa zunubi, Sai lokacin da ya ji da'awata, Har ya yanke mini shari'a. Zai kawo ni zuwa wurin haske, Zan kuwa ga cetonsa. 10 Sa'an nan maƙiyina wanda suke ce mini, “Ina Ubangiji Allahnka?” Zai gani, ya kuma ji kunya. Idanuna za su gan shi lokacin da aka tattake shi Kamar taɓo a titi. 11 Za a faɗaɗa iyakarka A ranar da za a gina garunka. 12 A waccan rana mutane za su zo wurinka, Daga Assuriya har zuwa Masar, Daga Masar zuwa Kogin Yufiretis, Daga teku zuwa teku, daga dutse zuwa dutse. 13 Duniya kuwa za ta zama kufai, Saboda mazaunan da suke cikinta, Saboda hakkin ayyukansu. Juyayin Ubangiji a kan Isra'ila 14 Sai ka yi kiwon mutanenka da sandanka, Wato garken mallakarka, Wanda yake zaune shi kaɗai a kurmi A tsakiyar ƙasa mai albarka. Bari su yi kiwo cikin Bashan da Gileyad Kamar a kwanakin dā. 15 “Zan nuna muku abubuwa masu banmamaki, Kamar a kwanakin da kuka fito ƙasar Masar.” 16 Al'umman duniya za su gani, Su kuwa ji kunyar ƙarfinsu duka. Za su sa hannuwansu a baka, Kunnuwansu za su kurmance. 17 Za su lashi ƙura kamar maciji da abubuwa masu rarrafe, Za su fito da rawar jiki daga wurin maɓuyarsu, Da tsoro za su juyo wurin Ubangiji Allahnmu, Za su ji tsoronka. 18 Akwai wani Allah kamarka, mai yafe mugunta, Mai kawar da laifin ringin gādonsa? Ba ya riƙon fushi har abada, gama shi mai alheri ne. 19 Zai sāke jin juyayinmu, Ya tattake muguntarmu a ƙarƙashin ƙafafunsa. Za ka jefar da zunubanmu a cikin zurfin teku. 20 Za ka nuna wa Yakubu aminci, Ga Ibrahim kuma madawwamiyar ƙauna, Kamar yadda ka rantse wa kakanninmu Tun a zamanin dā. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria