Mika 6 - Littafi Mai TsarkiUbangiji Yana Gāba da Isra'ila 1 “Ku ji abin da ni Ubangiji nake cewa, Tashi ku gabatar da ƙararku a gaban duwatsu, Ku bar tuddai su ji muryarku. 2 “Ku duwatsu da madawwaman tussan duniya, Ku ji tuhumar da Ubangiji yake yi muku. Gama Ubangiji, yana da magana gāba da mutanensa, Zai tuhumi Isra'ila. 3 “Ya ku jama'ata, me na yi muku? Wace irin fitina nake yi muku? Ku amsa mini! 4 Gama na fito da ku daga ƙasar Masar, Na fanshe ku daga gidan bauta. Na aika muku da Musa, da Haruna, da Maryamu. 5 Ya ku jama'ata, ku tuna Da abin da Balak, Sarkin Mowab, ya ƙulla, Da yadda Bal'amu ɗan Beyor ya amsa masa, Da abin da ya faru daga Shittim, har zuwa Gilgal, Don ku san ayyukan adalci na Ubangiji.” Abin da Allah Yake So ga Mutane 6 Da me zan zo gaban Ubangiji, In sunkuyar da kaina a gaban Allah na Sama? Ko in zo gabansa da maraƙi bana ɗaya domin yin hadaya ta ƙonawa? 7 Ubangiji zai yi murna da raguna dubbai Ko kuwa da kogunan mai dubbai? Zan ba da ɗan farina ne don laifina? Ko kuwa zan ba da 'ya'yana saboda zunubina? 8 Ya kai mutum, ya riga ya nuna maka abin da yake mai kyau. Abin da Ubangiji yake so gare ka, shi ne Ka yi adalci, ka ƙaunaci aikata alheri, Ka bi Allah da tawali'u. 9 Ubangiji yana kira ga birnin. Hikima ce ƙwarai a ji tsoron sunanka. “Ki ji ya kabila, wa ya sa miki lokacinki? 10 Ba zan manta da dukiya ta mugunta a gidan mugu ba, Ba kuwa zan manta da bugaggen mudun awo ba. 11 Zan kuɓutar da mutum mai ma'auni na cuta Da ma'aunin ƙarya? 12 Attajiran birnin sun cika zalunci, Mazaunansa kuwa maƙaryata ne, Harshensu na yaudara ne. 13 Domin haka zan buge ku da ciwo, In maishe ku kufai saboda zunubanka. 14 Za ka ci, amma ba za ku ƙoshi ba, Yunwa za ta kasance a cikinku, Za ku tanada, amma ba zai tanadu ba, Abin da kuma kuka tanada zan bai wa takobi. 15 Za ku shuka, amma ba za ku girbe ba. Za ku matse 'ya'yan zaitun, amma ba za ku shafa mansa ba, Za ku kuma matse 'ya'yan inabi, amma ba za ku sha ruwansa ba. 16 Domin kun kiyaye dokokin Omri, Kun bi halin gidan Ahab, Kun kuma bi shawarwarinsu. Domin haka zan maishe ku kufai, In mai da ku abin dariya, Za ku sha raini a wurin mutanena.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria