Mika 5 - Littafi Mai Tsarki1 Ki tattara sojojinki, gama an kewaye mu da yaƙi. Za su bugi kumatun Sarkin Isra'ila da sanda. Mulkin Mai Ceto daga Baitalami 2 “Baitalami cikin Efrata, Wadda kike 'yar ƙarama a cikin kabilar Yahuza, Amma daga cikinki wani zai fito wanda zai sarauci Isra'ila Wanda asalinsa tun fil azal ne.” 3 Domin haka zai yashe su, Sai lokacin da wadda take naƙuda ta haihu. Sa'an nan sauran 'yan'uwansa Za su komo wurin mutanen Isra'ila. 4 Shi kuwa zai tashi ya ciyar da garkensa da ƙarfin Ubangiji, Da ɗaukakar sunan Ubangiji Allahnsa. Za su kuwa zauna lafiya, Gama zai zama mai girma cikin duniya duka. 5 Zai zama salamarmu. Sa'ad da kuma Assuriyawa za su kawo mana yaƙi, Za su tattake kagaranmu, Za mu sa makiyaya bakwai da shugabanni takwas su yi gāba da su. Ceto da Hukunci 6 Za su mallaki ƙasar Assuriya da takobi, Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod da zararren takobi, Zai cece mu daga hannun Ba'assuriye, Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmu yaƙi, Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu. 7 Sa'an nan ringin Yakubu zai zamar wa mutane Kamar raɓa daga wurin Ubangiji, Kamar kuma yayyafi a kan tsire-tsire, Wanda ba ya jinkiri ko ya jira mutane. 8 Ringin Yakubu kuma zai zamar wa al'umman duniya, Kamar yadda zaki yake a tsakanin namomin jeji, Kamar kuma yadda zaki yake a tsakanin garkunan tumaki, Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakan tattaka, Ya yi kacakaca da su, Ba wanda zai cece su. 9 Za a ƙarfafa hannunka a kan maƙiyanka, Za a datse maƙiyanka duka. 10 “A wannan rana, ni Ubangiji na ce, Zan kashe dawakanku, in hallaka karusanku. 11 Zan shafe biranen ƙasarku, In rushe garunku. 12 Zan kawar da maita daga ƙasarku, Ba za ku ƙara samun bokaye ba. 13 Zan sassare siffofinku da ginshiƙanku, Ba za ku ƙara sunkuya wa aikin hannuwanku ba. 14 Zan tumɓuke gumakan nan Ashtarot daga cikinku, Zan hallaka biranenku. 15 Da fushi da hasala zan yi sakayya A kan al'umman da ba su yi biyayya ba.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria