Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Mika 4 - Littafi Mai Tsarki


Mulkin Salama na Ubangiji
( Ish 2.1-4 )

1 Zai zama nan gaba, dutse inda Haikalin Ubangiji yake Zai zama shi ne mafi tsawo duka a cikin duwatsu, Zai fi tuddai tsayi, Mutane kuwa za su riƙa ɗunguma zuwa wurinsa.

2 Al'umman duniya za su zo, su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa Haikalin Allah na Isra'ila, Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa.” Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.

3 Zai shara'anta tsakanin al'umman duniya masu yawa, Zai sulhunta jayayyar da take tsakanin manyan al'ummai, Za su mai da takubansu garemani, Māsunsu kuma su maishe su wuƙaƙen aske itace. Al'umma ba za ta ƙara fita zuwa yaƙi ba, Ba za su ƙara koyon yaƙi ba.

4 Kowa zai zauna gindin kurangar inabinsa da gindin ɓaurensa. Ba wanda zai tsoratar da shi, Gama Ubangiji Mai Runduna ne ya faɗa.

5 Ko da yake al'ummai suna bin gumakansu, Amma mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.


Kuɓutar Isra'ila daga Zaman Talala

6 Ubangiji ya ce, “A waccan rana zan tattara guragu, Da waɗanda aka kora, Da waɗanda na wahalshe su.

7 Zan sa guragu su wanzu, Korarru kuwa su zama al'umma mai ƙarfi, Ni, Ubangiji, zan yi mulkinsu a Sihiyona har abada.

8 “Ke kuma hasumiyar garken tumaki, tudun Sihiyona, Mulki na dā zai komo wurinki, Wato sarautar Urushalima.”

9 Yanzu, me ya sa kike kuka da ƙarfi? Ba sarki a cikinki ne? Mashawarcinki ya hallaka ne, Da azaba ta auka miki kamar ta mace mai naƙuda?

10 Ki yi makyarkyata, ki yi nishi, ke Sihiyona, Kamar mace mai naƙuda, Gama yanzu za ki fita daga cikin birni, Ki zauna a karkara, Za ki tafi Babila, daga can za a cece ki. Daga can Ubangiji zai cece ki daga hannun maƙiyanki.

11 Yanzu al'ummai sun taru suna gāba da ke, suna cewa, “Bari a ƙazantar da ita, Bari mu zura mata ido.”

12 Amma ba su san nufin Ubangiji ba, Ba su gane shirinsa ba, Gama ya tara su ne kamar dammunan da za a kai masussuka.

13 “Ya Sihiyona, ki tashi, ki tattaka! Gama zan mai da ƙahonki ƙarfe, kofatanki kuwa tagulla, Za ki ragargaje al'ummai da yawa.” Za ki ba Ubangijin dukan duniya dukiyarsu da suka tara ta hanyar zamba, Wadatarsu kuma ga Ubangijin dukan duniya.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan