Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Mika 2 - Littafi Mai Tsarki


Taku ta Ƙare, Ku Masu Zaluntar Matalauta

1 Taku ta ƙare, ku masu shirya mugunta, Masu tsara mugunta a gadajensu! Sa'ad da gari ya waye, sai su aikata ta, Domin ikon aikatawa yana hannunsu.

2 Sukan yi ƙyashin gonaki da gidaje, sai su ƙwace. Sukan zalunci mutum, su ƙwace gidansa da gādonsa.

3 Domin haka Ubangiji ya ce, Ga shi, yana shirya wa wannan jama'a masifa, Wadda ba za ku iya kuɓuta daga cikinta ba. Ba kuma za ku yi tafiyar alfarma ba, Gama mugun lokaci ne.

4 A wannan rana za su yi karin magana a kanku, Za su yi kuka da baƙin ciki mai zafi, Su ce, “An lalatar da mu sarai! Ya sāke rabon mutanena, Ya kawar da shi daga gare ni! Ya ba da gonakinmu ga waɗanda suka ci mu da yaƙi.”

5 Don haka ba za ku sami wanda zai sa muku ma'auni A taron jama'ar Ubangiji ba.

6 “Kada su yi wa'azi,” amma sun yi wa'azi. “Idan ba su yi wa'azi a kan abubuwan nan ba, Raini ba zai ƙare ba.

7 Daidai ne a faɗi haka, ya jama'ar Yakubu? ‘Ruhun Ubangiji ya yi rashin haƙuri ne? Waɗannan ayyukansa ne?’ ” “Ashe, maganata ba takan amfana wanda yake tafiya daidai ba?”

8 Ubangiji ya amsa ya ce, “Ba da daɗewa ba mutanena sun tashi kamar maƙiyi, Kukan tuɓe rigar masu wucewa da salama, masu komawa da yaƙi.

9 Kukan kori matan mutanena Daga gidajensu masu kyau, Kukan kawar da darajata har abada daga wurin 'ya'yansu.

10 Ku tashi, ku tafi, Gama nan ba wurin hutawa ba ne, Saboda ƙazantarku wadda take kawo muguwar hallaka.

11 “Idan mutum ya tashi yana iskanci, yana faɗar ƙarya, ya ce, ‘Zan yi muku wa'azi game da ruwan inabi da abin sa maye,’ To, shi ne zai zama mai wa'azin mutanen nan!

12 “Hakika zan tattara ku duka, ya Yakubu, Zan tattara ringin Isra'ila. Zan haɗa su tare kamar tumaki a garke, Kamar garken tumaki a makiyaya Za su zama taron jama'a mai hayaniya.

13 “Wanda zai huda garu, shi zai yi musu jagora, Za su fita ƙofar, su wuce, su fice ta cikinta. Sarkinsu zai wuce gabansu, Ubangiji kuma yana kan gaba.”

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan