Mika 1 - Littafi Mai Tsarki1 Ubangiji ya yi magana da Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da na Hezekiya, sarakunan Yahuza. Ya yi masa magana a kan Samariya da Urushalima. Makoki don Samariya da Urushalima 2 Dukanku ku ji, ku al'ummai! Ki kasa kunne, ya duniya, da dukan abin da yake cikinki. Bari Ubangiji Allah Daga Haikalinsa mai tsarki ya zama shaida a kanku. 3 Ga shi, Ubangiji yana fitowa daga wurin zamansa, Zai sauko, ya taka kan tsawawan duwatsun duniya. 4 Duwatsu za su narke a ƙarƙashinsa, Kwaruruka za su tsattsage kamar kakin zuma a gaban wuta, Kamar ruwa yana gangarowa daga tsauni. 5 Duk wannan kuwa saboda laifin Yakubu ne, Da laifin Isra'ila. Mene ne laifin Yakubu? Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin da ake yi a Samariya ba? Mene ne kuma laifin Yahuza? Ashe, ba bautar gumaka da zaluncin da ake yi a Urushalima ba? 6 “Domin haka zan mai da Samariya jujin kufai a karkara, Wurin dasa kurangar inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari, In tone harsashin gininta. 7 Za a farfashe dukan siffofinta na zubi, Za a ƙaƙƙone dukiyarta da wuta, Zan lalatar da gumakanta duka, Gama ta wurin karuwanci ta samo su, Ga karuwanci kuma za su koma.” 8 Mika ya ce, “Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka, Zan tuɓe, in yi tafiya huntu. Zan yi kuka kamar diloli, In yi baƙin ciki kamar jiminai. 9 Gama raunin Samariya, ba ya warkuwa, Gama ya kai Yahuza, Ya kuma kai ƙofar jama'ata a Urushalima.” 10 Kada a faɗe shi a Gat, Sam, kada a yi kuka. Yi birgima cikin ƙura a Bet-leyafra. 11 Ku mazaunan Shafir, ku wuce abinku da tsiraici da kunya. Mazaunan Za'anan ba su tsira ba. Bet-ezel ta yi kururuwa, “Zai tumɓuke harasashin gininki.” 12 Mutanen Marot sun ƙosa su ga alheri, Amma masifa ta zo ƙofar Urushalima daga wurin Ubangiji. 13 Ku mutanen Lakish, ku ɗaura wa dawakai karusai, Gama ku kuka fara yin zunubi a Sihiyona, Gama an iske laifofin Isra'ila cikinku. 14 Domin haka sai ku ba Moreshet-gat guzuri, Mutanen Akzib za su yaudari sarakunan Isra'ila. 15 Ku mazaunan Maresha, Ubangiji zai kawo wanda zai ci ku da yaƙi, Darajar Isra'ila za ta shiga Adullam. 16 Ku aske kanku saboda ƙaunatattun 'ya'yanku. Ku yi wa kanku ƙwaƙwal kamar ungulu, Gama 'ya'yanku za su tafi bautar talala. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria