Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ƙidaya 7 - Littafi Mai Tsarki


Hadayun Keɓe Bagade

1 A ranar da Musa ya gama kafa alfarwa ta sujada, ya shafa mata mai, ya tsarkake ta, da dukan kayayyakinta, ya kuma shafa wa bagaden mai, ya tsarkake shi da dukan kayayyakinsa.

2 Sai shugabannin Isra'ila, wato shugabannin gidajen kakanninsu, su ne shugabannin kabilansu, waɗanda suka shugabanci waɗannan da aka ƙidaya,

3 suka kawo hadayarsu a gaban Ubangiji, karusai shida rufaffu, da takarkarai goma sha biyu. Shugabanni biyu suka ba da karusa ɗaya, kowannensu kuwa ya ba da takarkari ɗaya, da suka gama miƙa su,

4 sai Ubangiji ya ce wa Musa,

5 “Karɓi waɗannan daga gare su domin a yi aiki da su a alfarwa ta sujada. Ka ba da su ga Lawiyawa, a ba kowane mutum bisa ga aikinsa.”

6 Musa kuwa ya karɓi karusan, da takarkaran, ya ba Lawiyawa.

7 Ya ba 'ya'ya maza na Gershon karusai biyu da takarkarai huɗu bisa ga aikinsu.

8 Ya kuwa ba 'ya'ya maza na Merari karusai huɗu da takarkarai takwas bisa ga aikinsu, a hannun Itamar ɗan Haruna, firist.

9 Amma bai ba 'ya'ya maza na Kohat kome ba, domin aikinsu shi ne lura da kayayyaki masu tsarki waɗanda ake ɗauka a kafaɗa.

10 Sai shugabanni suka miƙa hadayu domin keɓewar bagade a ranar da aka zuba masa mai. Suka fara miƙa sadakokinsu a bagaden,

11 Ubangiji kuma ya ce wa Musa, “Bari shugabannin su kawo hadayunsa domin keɓewar bagade, har kwana sha biyu, kowa a ranarsa.”

12-83 Suka miƙa hadayunsu bi da bi kamar haka, Rana Kabila Shugaba Rana ta farko Yahuza Nashon ɗan Amminadab Rana ta biyu Issaka Netanel ɗan Zuwar Rana ta uku Zabaluna Eliyab ɗan Helon Rana ta huɗu Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur Rana ta biyar Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai Rana ta shida Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel Rana ta bakwai Ifraimu Elishama ɗan Ammihud Rana ta takwas Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur Rana ta tara Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni Rana ta goma Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai Rana ta goma sha ɗaya Ashiru Fagiyel ɗan Okran Rana ta goma sha biyu Naftali Ahira ɗan Enan Hadayun da kowannensu ya kawo duk daidai da juna suke, farantin azurfa na shekel ɗari da talatin, da kwanon azurfa na shekel saba'in, bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi, duka suna cike da garin da aka kwaɓa da mai domin hadaya ta gari, cokali na zinariya guda na shekel goma, cike da kayan ƙanshi, da ɗan bijimi guda, da rago ɗaya, da ɗan rago bana ɗaya domin hadaya ta ƙonawa, da akuya guda domin hadaya ta zunubi, da bijimai biyu, da raguna biyar, da awaki biyar, da 'yan raguna biyar bana ɗaya ɗaya, domin hadaya ta salama.


Rana Kabila Shugaba

84-88 Ga jimillar hadayun da shugabanni goma sha biyu suka kawo domin keɓewar bagaden: farantan azurfa goma sha biyu da kwanonin azurfa goma sha biyu, duka nauyinsu shekel dubu biyu da ɗari huɗu cokulan zinariya goma sha biyu, nauyinsu duka shekel ɗari da ashirin cike da kayan ƙanshi bijimai goma sha biyu, da raguna goma sha biyu, da 'yan raguna goma sha biyu bana ɗaya ɗaya, da kuma hadaya ta gari da za a haɗa da waɗannan domin hadaya ta ƙonawa awaki goma sha biyu domin hadaya don zunubi bijimai ashirin da huɗu, da raguna sittin, da awaki sittin, da 'yan raguna bana ɗaya ɗaya guda sittin domin hadaya ta salama.

89 Duk lokacin da Musa ya shiga alfarwa ta sujada domin ya yi magana da Ubangiji, sai ya ji Ubangiji yana magana da shi daga bisa murfin akwatin alkawari, a tsakanin kerubobi masu fikafikai biyu.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan