Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ƙidaya 2 - Littafi Mai Tsarki


Zango da Shugabannin Kabilai

1 Ubangiji ya ba Musa da Haruna waɗannan umarnai.

2 Duk sa'ad da Isra'ilawa suka yi zango, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Zangon zai kasance a kewaye da alfarwa ta sujada.

3-9 Ƙungiyoyin kabilar Yahuza za su sauka su kafa tutarsu a sashin gabas a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Yahuza Nashon ɗan Amminadab 74,600 Issaka Netanel ɗan Zuwar 54,400 Zabaluna Eliyab ɗan Helon 57,400 Jimilla duka 186,400 Ƙungiyoyin kabilar Yahuza su ne za su fara tafiya.


Kabila Shugaba Jimilla

10-16 Ƙungiyoyin kabilar Ra'ubainu za su sauka su kafa tutarsu a sashin kudu a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Ra'ubainu Elizur ɗan Shedeyur 46,500 Saminu Shelumiyel ɗan Zurishaddai 59,300 Gad Eliyasaf ɗan Deyuwel 45,650 Jimilla duka 151,450 Ƙungiyoyin kabilar Ra'ubainu za su bi bayan na Yahuza.


Kabila Shugaba Jimilla

17 Sa'an nan Lawiyawa ɗauke da alfarwa ta sujada za su kasance a tsakanin ƙungiyoyi biyu na farko da biyun da suke daga ƙarshe. Kowace ƙungiya za ta yi tafiya kamar yadda aka dokace ta ta zauna a zango, wato kowacce ta yi tafiya a ƙarƙashin tutarta a matsayinta.

18-24 Ƙungiyoyin kabilar Ifraimu za su sauka su kafa tutarsu a sashin yamma a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabilar Shugaba Jimilla Ifraimu Elishama ɗan Ammihud 40,500 Manassa Gamaliyel ɗan Fedazur 32,200 Biliyaminu Abidan ɗan Gideyoni 35,400 Jimilla duka 108,100 Ƙungiyoyin Ifraimu za su zama na uku a jerin.


Kabilar Shugaba Jimilla

25-31 Ƙungiyoyin kabilar Dan za su sauka su kafa tutarsu a sashin arewa a ƙarƙashin jagorancin shugabanninsu, kamar haka, Kabila Shugaba Jimilla Dan Ahiyezer ɗan Ammishaddai 62,700 Ashiru Fagiyel ɗan Okran 41,500 Naftali Ahira ɗan Enan 53,400 Jimilla duka 157,600 Ƙungiyoyin Dan za su bi daga bayan duka.


Kabila Shugaba Jimilla

32 Jimillar yawan Isra'ilawa da aka rubuta su a yadda suke ƙungiya ƙungiya, su dubu ɗari shida da uku da ɗari biyar da hamsin ne (603,550).

33 Amma kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa, ba a rubuta Lawiyawa haɗe da sauran Isra'ilawa ba.

34 Saboda haka Isra'ilawa suka yi dukan abin da Ubangiji ya umarci Musa. Kowa ya yi zango a ƙarƙashin tutarsa, kowa kuma ya yi tafiya cikin jerin kabilarsa.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan