Ishaya 12 - Littafi Mai TsarkiWaƙar Godiya 1 Rana tana zuwa sa'ad da jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ina yabonka ya Ubangiji! A dā ka yi fushi da ni, Amma yanzu kana yi mini ta'aziyya, ba za ka ƙara yin fushi da ni ba. 2 Allah ne Mai Cetona, Zan dogara gare shi, ba zan ji tsoro ba. Ubangiji ne yake ba ni iko da ƙarfi, Shi ne Mai Cetona.” 3 Kamar yadda ruwan daɗi yake sa mai jin ƙishirwa farin ciki, Haka nan jama'ar Allah suke farin ciki sa'ad da ya cece su. 4 A wannan rana jama'a za su raira waƙa, su ce, “Ku yi wa Ubangiji godiya! Ku nemi taimako a gare shi! Ku faɗa wa dukan sauran al'umma abin da ya aikata! Ku faɗa musu irin girman da yake da shi! 5 Ku raira waƙa ga Ubangiji, saboda manyan ayyuka da ya aikata. Bari dukan duniya ta ji labarin. 6 Bari dukan waɗanda suke zaune a Sihiyona su yi sowa su raira waƙa! Gama Mai Tsarki, Allah na Isra'ila, mai girma ne, Yana zaune tare da mutanensa.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria