Irmiya 6 - Littafi Mai TsarkiAjalin Urushalima da Yahuza 1 “Ya ku mutanen Biliyaminu, ku gudu neman mafaka, Daga cikin Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa, Ku ba da alama a Bet-akkerem, Gama masifa da babbar halaka sun fito daga arewa. 2 Ya Sihiyona, ke kyakkyawar makiyaya ce, zan hallaka abin da kika hahhaifa. 3 Makiyaya da garkunansu za su zo wurinki, Za su kafa alfarwansu kewaye da ke, Kowa zai yi kiwo a makiyayarki. 4 Za su ce, ‘Mu yi shiri mu fāɗa mata da yaƙi! Ku tashi, mu fāɗa musu da tsakar rana!’ Sai kuma suka ce, ‘Kaitonmu, ga rana tana faɗuwa, ta yi ruɗa-kuyangi. 5 Mu tashi mu fāɗa mata da dare, Mu lalatar da fādodinta.’ ” 6 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Ku sassare itatuwanta, Ku tula ƙasa kewaye da Urushalima, Dole in hukunta wannan birni saboda ba kome cikinsa sai zalunci, 7 Kamar yadda rijiya take da ruwa garau, Haka Urushalima take da muguntarta, Ana jin labarin kama-karya da na hallakarwa a cikinta, Kullum akwai cuce-cuce, da raunuka a gabana, 8 Ku ji faɗaka, ya ku mutanen Urushalima, Don kada a raba ni da ku, Don kada in maishe ku kufai, Ƙasar da ba mazauna ciki.” 9 Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Za a kalace ringin Isra'ila sarai, kamar yadda ake wa inabi, Ka miƙa hannunka a kan rassanta kamar mai tsinkar 'ya'yan inabi.” 10 Da wa zan yi magana don in faɗakar da shi, don su ji? Ga shi, kunnuwansu a toshe suke, su ji, Ga shi, maganar Ubangiji kuwa ta zama abin ba'a a gare su, Ba su marmarinta. 11-12 Don haka ina cike da fushin Ubangiji Na gaji da kannewa. Ubangiji ya ce, “Zan kwararo fushi kan yara da suke a titi. Da kuma kan tattaruwar samari. Za a ɗauke mata da miji duka biyu, Da tsofaffi, da waɗanda suka tsufa tukub-tukub. Za a ba waɗansu gidajensu, da gonakinsu, da matansu, Gama zan nuna ikona in hukunta mazaunan ƙasar. 13 Gama daga ƙaraminsu zuwa babba, Kowannensu yana haɗama ya ci ƙazamar riba, Har annabawa da firistoci, Kowannensu ya shiga aikata rashin gaskiya. 14 Sun warkar da raunin mutanena sama sama, Suna cewa, ‘Lafiya, Lafiya,’ alhali kuwa ba lafiya. 15 Sun ji kunya sa'ad da suka aikata abubuwan banƙyama? Ba su ji kunya ba ko kaɗan. Ko gezau ba su yi ba, Don haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a hamɓarar da su. Ni Ubangiji na faɗa.” 16 Haka Ubangiji ya ce, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba, Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, Ku bi ta, don ku hutar da rayukanku. Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’ 17 Na sa muku matsara cewa, in kun ji an busa ƙaho ku kula! Amma suka ce, ‘Ba za mu kula ba.’ 18 “Don haka, ku ji, ya ku al'ummai, Ku sani, ku taron jama'a, Don ku san abin da zai same ku. 19 Ki ji, ya ke duniya, Ga shi, ina kawo masifa a kan wannan jama'a, Sakayyar ƙulle-ƙullensu, Don ba su kula da maganata ba, Sun ƙi dokokina. 20 Da wane nufi kuke kawo mini turare daga Sheba, Ko raken da kuke kawowa daga ƙasa mai nisa? Ba zan karɓi hadayunku na ƙonawa ba, Ba kuwa zan ji daɗin sadakokinku ba. 21 Don haka, ni Ubangiji na ce, Zan sa abin tuntuɓe a gaban wannan jama'a, Za su kuwa yi tuntuɓe, su fāɗi. Iyaye tare da 'ya'yansu, da maƙwabci, Do abokansu za su lalace.” 22 Haka Ubangiji ya ce, “Ga shi, jama'a tana fitowa daga ƙasar arewa. Babbar al'umma ce, Ta yunƙuro tun daga manisantan wurare na duniya. 23 Suna riƙe da baka da māshi, Mugaye ne marasa tausayi, Motsinsu kamar ƙugin teku ne. Suna haye a kan dawakai, A jere kamar wanda ya yi shirin yaƙi Gāba da ke, ya 'yar Sihiyona.” 24 Mutanen Urushalima sun ce, “Mun ji labarin yaƙin, Hannuwanmu suka yi rauni. Azaba ta kama mu, Ciwo irin na mai naƙuda. 25 Kada ku fita zuwa gona, Kada kuma ku yi yawo a kan hanya, Gama abokin gāba yana da takobi, Razana a kowane sashi.” 26 “Ya mutanena, ku sa tufafin makoki, Ku yi birgima cikin toka, Ku yi makoki mai zafi irin wanda akan yi wa ɗa tilo, Gama mai hallakarwa zai auko mana nan da nan.” 27 Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Na maishe ka mai aunawa da mai jarraba mutanena Domin ka sani, ka auna al'amuransu, 28 Su duka masu taurinkai ne, 'yan tawaye, Suna yawo suna baza jita-jita. Su tagulla ne da baƙin ƙarfe, Dukansu lalatattu ne. 29 Ana zuga da ƙarfi, Dalma ta ƙone, Tacewar aikin banza ne, Gama ba a fitar da mugaye ba. 30 Ana ce da su ƙwan maƙerar azurfa ne, Gama ni na ƙi su.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria