Irmiya 51 - Littafi Mai TsarkiHukuncin Ubangiji a kan Babila 1 Ubangiji ya ce, “Ga shi, zan kawo iskar ɓarna a kan Babila Da mazaunan Kaldiya. 2 Zan aika da masu casawa zuwa Babila, za su casa ta, Su bar ƙasarta kango. Za su kewaye ta a kowane sashi A wannan ranar masifa. 3 Kada ku bar maharbi ya yi harbi da bakansa, Kada kuma ya sa kayan yaƙinsa, Kada ku rage samarinta, Ku hallaka dukan sojojinta. 4 Za su fāɗi matattu a ƙasar Kaldiyawa, Za a sassoke su a titunansu.” 5 Allah na Isra'ila da Yahuza, Ubangiji Mai Runduna, bai yashe su ba, Ko da yake sun yi wa Mai Tsarki na Isra'ila zunubi. 6 Ku gudu daga cikin Babila, Bari kowa ya ceci ransa, Kada a hallaka ku tare da ita, Gama a wannan lokaci Ubangiji zai sāka mata, Zai sāka mata bisa ga alhakinta. 7 Babila ta zama ƙoƙon zinariya a hannun Ubangiji, Ta sa dukan duniya ta yi maye. Ƙasashen duniya sun sha ruwan inabinta, suka haukace. 8 Farat ɗaya, Babila ta fāɗi, ta kakkarye, Ku yi kuka dominta! Ku samo mata magani domin azabar da take sha, watakila ta warke. 9 Mun ba Babila magani, amma ba ta warke ba. Bari mu ƙyale ta, kowannenmu ya koma garinsu, Gama hukuncinta ya kai sammai, ya yi tsawo har samaniya. 10 Ubangiji ya baratar da mu a fili, Bari mu tafi mu yi shelar aikin Ubangiji Allahnmu a cikin Sihiyona. 11 Ku wasa kibau, ku cika kwaruruwanku! Ubangiji ya ta da ruhun sarakunan Mediyawa, Domin yana niyyar hallaka Babila. Gama Ubangiji zai yi ramuwa saboda Haikalinsa. 12 Ku ta da tuta don a faɗa wa garun Babila, Ku ƙarfafa matsara, Ku sa su su yi tsaro, Ku kuma sa 'yan kwanto! Ga shi, Ubangiji ya yi niyya, ya kuwa aikata Abin da ya faɗa a kan mazaunan Babila. 13 Ƙarshenki ya zo, Ke mai zama kusa da ruwa mai yawa, Mai yawan dukiya. Ajalinki ya auka. 14 Ubangiji Mai Runduna ya rantse da zatinsa, ya ce, “Hakika zan cika Babila da mutane kamar fāra, Za su kuwa raira waƙar nasara a kanta.” 15 Ubangiji ne ya halicci ƙasa da ikonsa, Ya kafa duniya da hikimarsa, Ya kuma shimfiɗa sammai da fahiminsa. 16 Bisa ga umarninsa ruwan da yake samaniya yakan yi ruri, Yakan sa gajimare su tashi daga ƙarshen duniya, Yakan sa walƙiya ta walƙata cikin ruwan sama, Yakan sa iska ta haura daga cikin taskokinsa. 17 Kowane ɗan adam wawa ne, marar ilimi, Kowane maƙerin zinariya kuma zai sha kunya daga wurin gumakansa, Gama siffofinsa na ƙarya ne, ba numfashi a cikinsu. 18 Su marasa amfani ne, aikin ruɗarwa ne kawai, Za su lalace a lokacin da za a hukunta su. 19 Amma wanda yake wajen Yakubu ba haka yake ba, Domin shi ne ya halicci dukan abu, Isra'ila kuwa abin mallakarsa ne, Ubangiji Mai Runduna ne sunansa. 20 Ubangiji ya ce, “Kai ne guduma da kayan yaƙina, Da kai ne na farfasa ƙasashen duniya, Da kai ne na hallaka mulkoki. 21 Da kai ne na karya doki da mahayinsa, 22 Da kai ne na farfasa karusa da mahayinsa. Da kai ne na kakkarya mace da namiji, Da kai ne na kakkarya tsoho da saurayi, Da kai ne na kakkarya saurayi da budurwa, 23 Da kai ne na kakkarya makiyayi da garkensa, Da kai ne na kakkarya manoma da dawakan nomansa, Da kai ne na kakkarya masu mulki da shugabanni.” 24 Ubangiji ya ce, “Zan sāka wa Babila da dukan mazaunan Kaldiya a ganin idanunku saboda dukan muguntar da suka aikata a Sihiyona. 25 “Ga shi, ina gaba da kai, ya dutse mai hallakarwa, Wanda ya hallaka duniya duka. Zan miƙa hannuna gāba da kai, Zan mirgino da ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, Zan maishe ka ƙonannen dutse. 26 Ba za a sami dutsen yin kusurwa, ko na kafa harsashen gini a cikinka ba, Amma za ka zama marar amfani har abada.” 27 Ku ta da tuta a duniya, Ku busa wa ƙasashen duniya ƙaho, Ku shirya ƙasashe don su yi yaƙi da ita, Ku kirawo mulkokin Ararat, da na Minni, da na Ashkenaz, su yi yaƙi da ita. Ku naɗa sarkin yaƙi wanda zai shugabanci yaƙin da za a yi da ita, Ku kawo dawakai kamar fāra. 28 Ku shirya ƙasashe su yi yaƙi da ita, Sarakunan Mediyawa, da masu mulkinsu, da shugabanninsu, Da kowace ƙasar da take ƙarƙashin mulkinsu. 29 Duniya ta girgiza, tana makyarkyata saboda azaba, Gama nufin Ubangiji na gāba da Babila ya tabbata, Nufinsa na mai da ƙasar Babila kufai, inda ba kowa. 30 Sojojin Babila sun daina yaƙi, suna zaune a cikin kagaransu. Ƙarfinsu ya ƙare, sun zama mata, An sa wa wuraren zamanta wuta, An karya ƙyamaren ƙofofin garinta. 31 Maguji yana biye da maguji a guje, Jakada yana biye da jakada, Don su faɗa wa Sarkin Babila, cewa an ci birninsa a kowane gefe. 32 An ƙwace mashigai An ƙone fadamu da wuta, Sojoji sun gigice. 33 Ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, “Mutanen Babila sun zama kamar daɓen masussuka A lokacin da ake sussuka, Ba kuwa da daɗewa ba lokacin girbe ta zai zo.” 34 Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya cinye Urushalima, Ya ragargaza ta, Ya maishe ta kufai, Ya haɗiye ta kamar yadda dodon ruwa yakan yi, Ya cika cikinsa da kayan marmarinta, Ya tatse ta sarai. 35 Bari mutanen Sihiyona su ce, “Allah ya sa muguntar da mutanen Babila suka yi mana ta koma kansu!” Bari kuma mutanen Urushalima su ce, “Allah ya sa hakkin jininmu ya koma kan Kaldiyawa!” 36 Ubangiji ya ce, “Zan tsaya muku, Zan ɗaukar muku fansa, Zan sa tekunsu da maɓuɓɓugarsu su ƙafe. 37 Babila za ta zama tarin juji, wurin zaman diloli, Abar ƙyama da abar ba'a, inda ba kowa. 38 Mutanen Babila za su yi ruri kamar zakuna, Su yi gurnani kamar 'ya'yan zaki. 39 Sa'ad da suke cike da haɗama zan yi musu biki, In sa su sha, su yi maye, su yi murna. Za su shiga barcin da ba za su farka ba. 40 Zan kai su mayanka kamar 'yan raguna, da raguna, da bunsurai. 41 “An ci Babila, Ita wadda duniya duka take yabo an cinye ta da yaƙi, Ta zama abar ƙyama ga sauran al'umma! 42 Teku ta malalo a kan Babila, Raƙuman ruwa masu hauka sun rufe ta. 43 Garuruwanta sun zama abin ƙyama, Ta zama hamada, inda ba ruwa, Ƙasar da ba mazauna, Ba kuma mutumin da zai ratsa ta cikinta. 44 Zan hukunta Bel, gunkin Babila, Zan sa ya yi aman abin da ya haɗiye, Ƙasashen duniya ba za su ƙara bumbuntowa wurinsa ba. Garun Babila ya rushe!” 45 “Ku fito daga cikinta, ya jama'ata, Kowa ya tsere da ransa daga zafin fushin Ubangiji. 46 Kada zuciyarku ta yi suwu, Kada kuma ku ji tsoro saboda labarin da ake ji a ƙasar, Labari na wannan shekara dabam, na wancan kuma dabam, A kan hargitsin da yake a ƙasar, Mai mulki ya tasar wa mai mulki. 47 Saboda haka kwanaki suna zuwa, Sa'ad da zan hukunta gumakan Babila, Za a kunyatar da dukan ƙasar Babila, Dukan matattunta za su faɗi a tsakiyarta. 48 Sa'an nan sama da duniya, da dukan abin da take cikinsu, Za su raira waƙar farin ciki, Domin masu hallakarwa daga arewa da za su auko mata, Ni Ubangiji na faɗa.” 49 Babila za ta fāɗi, Saboda mutanen Isra'ila da dukan mutanen duniya waɗanda ta kashe. 50 Ku waɗanda kuka tsere wa takobi! Ku gudu! Kada ku tsaya! Ku tuna da Ubangiji a can nesa inda kuke, Ku kuma yi ta tunawa da Urushalima. 51 Mun sha kunya saboda zargin da ake yi mana, Kunya ta rufe mu, Gama baƙi sun shiga tsarkakan wurare na Haikalin Ubangiji. 52 “Domin haka kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “Sa'ad da zan hukunta gumakan Babila, da dukan ƙasarta, Waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi. 53 Ko da Babila za ta hau samaniya, Ta gina kagara mai ƙarfi a can, Duk da haka zan aiki masu hallakarwa a kanta, Ni Ubangiji na faɗa.” 54 Ku ji muryar kuka daga Babila, Da hargowar babbar hallakarwa daga ƙasar Kaldiyawa! 55 Gama Ubangiji yana lalatar da Babila, Yana kuma sa ta kame bakinta na alfarma, Sojoji suna kutsawa kamar raƙuman ruwa, Suna ta da muryoyinsu. 56 Gama mai hallakarwa ya auka wa Babila, An kama sojojinta, An kuma kakkarya bakunansu, Gama Ubangiji shi Allah ne, mai sakayya, Zai yi sakayya sosai. 57 “Zan sa mahukuntanta, da masu hikimarta, Da masu mulkinta, da shugabanninta, Da sojojinta su sha su yi maye. Za su dinga yin barcin da ba za su farka ba,” In ji Sarkin, mai suna Ubangiji Mai Runduna. 58 “Ni Ubangiji Mai Runduna, na ce, Za a baje garun nan na Babila mai fāɗi Za a kuma ƙone dogayen ƙyamarenta da wuta. Mutane sun wahalar da kansu a banza. Sauran al'umma sun yi wahala kawai domin wutar lalata.” 59 Jawabin da annabi Irmiya ya ba Seraiya, ɗan Neriya, wato jikan Ma'aseya, lokacin da ya tafi tare da Zadakiya, Sarkin Yahuza, zuwa Babila a shekara ta huɗu ta mulkinsa. Seraiya shi ne shugaba mai lura da gidajen saukar baƙi. 60 Irmiya ya rubuta a littafi dukan masifun da za su auko wa Babila, wato dukan wannan magana da aka rubuta a kan Babila. 61 Irmiya kuwa ya ce wa Seraiya, “Lokacin da ka kai Babila, sai ka karanta dukan maganan nan. 62 Ka kuma ce, ‘Ya Ubangiji, kai ne ka yi magana a kan wannan wuri, cewa za ka lalatar da shi, har ba abin da zai zauna a ciki, mutum ko dabba. Wurin zai zama kufai har abada.’ 63 Sa'ad da ka gama karanta wannan littafi, sai ka ɗaura wa littafin dutse, sa'an nan ka jefar da shi tsakiyar Kogin Yufiretis. 64 Sa'an nan ka ce, ‘Haka Babila za ta nutse, ba za ta ƙara tashi ba saboda masifar da Ubangiji zai kawo mata.’ ” Wannan shi ne ƙarshen maganar Irmiya. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria