Irmiya 50 - Littafi Mai TsarkiJawabin Ubangiji a kan Babila 1 Jawabin da Ubangiji ya yi wa annabi Irmiya a kan Babila da ƙasar Kaldiyawa ke nan, 2 “Ku ba da labari ga sauran al'umma, ku yi shela, Ku ta da tuta, ku yi shela, Kada ku ɓuya, amma ku ce, ‘An ci Babila da yaƙi, An kunyatar da Bel, An kunyatar da siffofinta, Merodak ya rushe, Gumakanta kuma sun ragargaje!’ 3 “Wata al'umma za ta taso daga arewa gāba da ita, za ta mai da ƙasar abar ƙyama, ba wanda zai zauna ciki. Mutum da dabba duk sun watse, kowa ya bar ta.” 4 Ubangiji ya ce, “Sa'ad da lokacin nan ya yi, mutanen Isra'ila da na Yahuza za su zo tare, suna kuka, suna nemana, ni Ubangiji Allahnsu. 5 Za su tambayi hanyar Sihiyona, sa'an nan su bi ta, suna cewa, ‘Bari mu haɗa kanmu don mu yi madawwamin alkawari da Ubangiji, alkawari wanda ba za a manta da shi ba.’ 6 “Mutanena sun zama kamar ɓatattun tumaki, Waɗanda makiyayansu suka bauɗar da su, Suka ɓata a cikin tsaunuka, Suna kai da kawowa daga wannan dutse zuwa wancan. Sun manta da shingensu. 7 Duk waɗanda suka same su, sun cinye su. Maƙiyansu suka ce, ‘Ba mu yi laifi ba,’ Gama sun yi wa Ubangiji laifi, wanda yake tushen gaskiya, Ubangiji wanda kakanninsu suka dogara gare shi. 8 “Ku gudu daga cikin Babila, Ku fita kuma daga cikin ƙasar Kaldiyawa, Ku zama kamar bunsurai waɗanda suke ja gaban garke. 9 Ga shi, zan kuta manyan ƙasashe daga arewa Su faɗa wa Babila da yaƙi. Za su ja dāgar yaƙi gāba da ita, su cinye ta. Kibansu kamar na gwanayen mayaƙa ne Waɗanda ba su komowa banza. 10 Za a washe Kaldiyawa, Waɗanda suka washe su kuwa za su ƙoshi, Ni Ubangiji na faɗa. 11 “Saboda kuna murna, kuna farin ciki, Ku da kuka washe gādona, Saboda kuma kuna tsalle kamar karsana a cikin ciyawa, Kuna haniniya kamar ingarmu, 12 Domin haka za a kunyatar da Babila sosai, inda kuka fito. Za ta zama ta baya duka a cikin sauran al'umma, Za ta zama hamada, busasshiyar ƙasa. 13 Saboda fushin Ubangiji, ba wanda zai zauna a cikinta, Za ta zama kufai, Duk wanda ya bi ta wajen Babila, zai ji tsoro, Zai kuma yi tsaki saboda lalacewarta. 14 “Dukanku 'yan baka, ku ja dāga, ku kewaye Babila, Ku harbe ta, kada ku rage kibanku, Gama ta yi wa Ubangiji zunubi. 15 Ku kewaye ta da kuwwar yaƙi! Ta ba da gari, Ginshiƙanta sun fāɗi. An rushe garunta, Gama wannan sakayya ce ta Ubangiji. Ku sāka mata, ku yi mata kamar yadda ta yi. 16 Ku datse wa Babila mai shuka, Da mai yanka da lauje a lokacin girbi. Saboda takobin azzalumi, Kowa zai koma wurin mutanensa, Kowa kuma zai gudu zuwa ƙasarsa.” 17 “Isra'ilawa kamar tumaki ne waɗanda zakuna suka bi su suna kora. Da farko dai Sarkin Assuriya ne ya cinye su. Yanzu kuwa Sarkin Babila, wato Nebukadnezzar, shi ne yake gaigayi ƙasusuwansu. 18 Saboda haka ni Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila na ce, zan yi wa Sarkin Babila da ƙasarsa hukunci, kamar yadda na hukunta Sarkin Assuriya. 19 Zan komar da Isra'ila a makiyayarsa, zai yi kiwo a Karmel da Bashan. Zai sami biyan bukatarsa a tsaunukan Ifraimu da na Gileyad. 20 Ni Ubangiji na ce sa'ad da lokacin nan ya yi za a nemi laifi da zunubi a cikin Isra'ila da Yahuza, amma ba za a samu ba, gama zan gafarta wa sauran da suka ragu. 21 “Ku haura ku fāɗa wa ƙasar Meratayim da mazaunan Fekod. Ku kashe, ku hallaka su sarai, Ku aikata dukan abin da na umarce ku, Ni Ubangiji na faɗa. 22 Hargowar yaƙi tana cikin ƙasar, Da kuma babbar hallakarwa! 23 Ga yadda aka karya gudumar dukan duniya! Ga yadda Babila ta zama abar ƙyama ga sauran al'umma! 24 Na kafa miki tarko, ya kuwa kama ki, ya Babila, Ke kuwa ba ki sani ba. An same ki, an kama, Domin kin yi gāba da ni.” 25 Ubangiji ya buɗe taskar makamansa, Ya fito da makaman hasalarsa, Gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana da aikin da zai yi a ƙasar Kaldiyawa. 26 Ku zo, ku fāɗa mata daga kowane sashi. Ku buɗe rumbunanta, Ku tsittsiba ta kamar tsibin hatsi, Ku hallakar da ita ɗungum, Kada wani abu nata ya ragu. 27 Ku kashe dukan bijimanta, a kai su mayanka! Kaitonsu, gama kwanansu ya ƙare, Lokacin hukuncinsu ya yi. 28 Ku ji, sun gudu sun tsere daga ƙasar Babila, Don su faɗa cikin Sihiyona, Sakayyar Ubangiji Allahnmu domin Haikalinsa. 29 “Ku kirawo 'yan baka, dukan waɗanda sukan ja baka, su faɗa wa Babila. Ku kafa sansani kewaye da ita, kada ku bar kowa ya tsira. Ku sāka mata bisa ga dukan ayyukanta, gama ta raina Ubangiji Mai Tsarki na Isra'ila. 30 Domin haka samarinta za su fāɗi a tituna. Za a hallaka sojojinta duka a wannan rana, Ni Ubangiji na faɗa. 31 “Ga shi, ina gāba da ke, ke Babila, mai girmankai. Gama ranar da zan hukunta ki, ta zo, Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa. 32 Mai girmankai za ta yi tuntuɓe ta fāɗi, Ba kuwa wanda zai tashe ta, Zan ƙone garuruwanta da wuta, Zan kuma hallaka dukan abin da yake kewaye da ita. 33 “Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, An danne mutanen Isra'ila da na Yahuza, Duk waɗanda suka kama su bayi sun riƙe su da ƙarfi. Sun ƙi su sake su. 34 Mai fansarsu mai ƙarfi ne, Ubangiji Mai Runduna ne sunansa. Hakika zai tsaya musu don ya kawo wa duniya salama, Amma zai kawo wa mazaunan Babila fitina. 35 Ni Ubangiji na ce, Akwai takobi a kan Kaldiyawa, Da a kan mazaunan Babila, Da a kan ma'aikatanta da masu hikimarta, 36 Akwai takobi a kan masu sihiri Don su zama wawaye. Akwai takobi a kan jarumawanta Don a hallaka su. 37 Akwai takobi a kan mahayan dawakanta, da a kan karusanta, Da a kan sojojin da ta yi ijara da su Don su zama kamar mata, Akwai takobi a kan dukan dukiyarta domin a washe ta. 38 Fari zai sa ruwanta ya ƙafe, Gama ƙasa tana cike da gumaka waɗanda suka ɗauke hankalin mutane. 39 “Domin haka namomin jeji da diloli za su zauna a Babila, Haka kuma jiminai. Ba za a ƙara samun mazauna a cikinta ba har dukan zamanai. 40 Abin da ya faru da Saduma da Gwamrata, Da biranen da suke kewaye da su, Shi ne zai faru da Babila. Ba mutumin da zai zauna cikinta. 41 “Ga mutane suna zuwa daga arewa, Babbar al'umma da sarakuna Suna tahowa daga wurare masu nisa na duniya. 42 Suna riƙe da baka da māshi, Mugaye ne marasa tausayi. Amonsu yana kama da rurin teku, Suna shirya don yin yaƙi da ke, ya Babila. 43 Sarkin Babila ya ji labarinsu, Hannuwansa suka yi suwu. Wahala da azaba sun kama shi kamar mace mai naƙuda. 44 “Ni Ubangiji ina zuwa kamar zakin da yake fitowa daga kurmin Urdun zuwa makiyaya. Nan da nan zan sa su gudu daga gare ta. Sa'an nan zan naɗa mata wanda na zaɓa. Wa yake kama da ni? Wa zai yi ƙarata? Wane shugaba zai yi gāba da ni? 45 Saboda haka ku ji shirin da Ubangiji ya yi gāba da Babila, da nufin ya yi gaba da ƙasar Kaldiyawa. Hakika za a tafi da ƙananansu, garke zai zama kango. 46 Duniya za ta girgiza sa'ad da ta ji an ci Babila da yaƙi. Za a ji kukanta cikin sauran al'umma.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria