Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Irmiya 48 - Littafi Mai Tsarki


Jawabin Ubangiji a kan Mowab

1 Ga abin da Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila ya faɗa a kan Mowab, “Kaiton Nebo, gama ta lalace! An kunyatar da Kiriyatayim, an ci ta da yaƙi, An kunyatar da kagararta, an rushe ta.

2 Darajar Mowab ta ƙare. Ana shirya mata maƙarƙashiya a Heshbon, ‘Bari mu je mu ɓata ta daga zaman al'umma!’ Ke kuma Madmen za ki yi shiru, Takobi zai runtume ki.

3 Muryar kuka daga Horonayim tana cewa, ‘Risɓewa da babbar halaka!’

4 “An hallakar da Mowab, Ƙanananta suna kuka.

5 Gama a hawan Luhit, za su hau da kuka, Gama a gangaren Horonayim, Suna jin kukan wahalar halaka.

6 Ku gudu don ku tserar da rayukanku, Ku gudu kamar jakin jeji.

7 “Kun dogara ga ƙarfinku da wadatarku, Amma yanzu za a ci ku da yaƙi, Kemosh zai tafi bauta Tare da firistocinsa da shugabanninsa.

8 Mai hallakarwa zai shiga kowane gari, Don haka ba garin da zai tsira. Kwari da tudu za su lalace, Ni Ubangiji na faɗa.

9 Ku ba Mowab fikafikai, Gama za ta tashi ta gudu, Garuruwanta za su zama kango, Ba mazauna cikinsu.

10 “La'ananne ne shi wanda yake yin aikin Ubangiji da ha'inci, La'ananne ne shi kuma wanda ya hana wa takobinsa jini.

11 “Tun daga ƙuruciya Mowab tana zama lami lafiya, Hankali kwance, Ba a jujjuya ta daga tulu zuwa tulu ba, Ba a taɓa kai ta bauta ba, Domin haka daɗin ɗanɗanonta bai rabu da ita ba, Ƙanshinta kuma bai sāke ba.”

12 Ubangiji ya ce, “Domin haka kwanaki suna zuwa, sa'ad da zai aika da mutane su tuntsurar da tuluna, su zubar da ruwan inabi, su farfasa tulunanta.

13 Sa'an nan Kemosh zai kunyatar da Mowab, kamar yadda Betel wadda Isra'ilawa suka dogara gare ta ta kunyatar da su.

14 “Don me kake cewa, ‘Mu jarumawa ne, mayaƙan gaske?’

15 Mai hallaka Mowab da garuruwanta ya taho, Zaɓaɓɓun majiya ƙarfinta sun gangara mayanka, Ni sarki, mai suna Ubangiji Mai Runduna, na faɗa.

16 Masifar Mowab ta kusato, Halakarta kuma tana gaggabtowa.

17 “Ku yi makoki dominta, ku da kuke kewaye da ita, Dukanku da kuka san sunanta, ku ce, ‘Ƙaƙa sandan sarauta mai iko Da sanda mai daraja ya karye?’

18 Ku da kuke zaune a Dibon, Ku sauka daga wurin zamanku mai daraja, Ku zauna a busasshiyar ƙasa, Gama mai hallaka Mowab ya zo ya yi gab da ku. Ya riga ya rushe kagararku.

19 Ku mazaunan Arower, Ku tsaya a kan hanya, ku jira, Ku tambayi wanda yake gudu Da wanda yake tserewa, Abin da ya faru.

20 An kunyatar da Mowab, ta rushe. Ku yi kuka dominta, Ku faɗa a Arnon, cewa Mowab ta halaka.

21 “Hukunci ya auka kan garuruwan da suke a ƙasar fili, wato Holon, da Yahaza, da Mefayat,

22 da Dibon, da Nebo, da Bet-diblatayim,

23 da Kiriyatayim, da Bet-gamal, da Ba'almeyon,

24 da Kiriyot, da Bozara. Hukunci ya zo a kan dukan garuruwan Mowab na nesa da na kusa.

25 An karye ikon Mowab da ƙarfinta, ni Ubangiji na faɗa.

26 “Ku sa Mowab ta yi maye domin ta tayar wa Ubangiji. Za ta yi birgima cikin amanta, mutane kuwa za su yi dariya.

27 Kin yi wa mutanen Isra'ila dariya. A kowane lokacin da kika ambaci sunansu, sai ki taɗa kanki da raini kamar an kama su tare da ɓarayi.

28 “Ku mazaunan Mowab, ku bar garuruwanku, Ku tafi, ku zauna a kogwanni, Ku zama kamar kurciya wadda take yin sheƙarta a bakin kwazazzabo.

29 Mun ji labarin girmankan Mowab, da ɗaukaka kanta, Da alfarmarta, da izgilinta, Tana da girmankai ƙwarai.

30 Ni Ubangiji na san Mowab tana da girmankai, Alfarmarta ta banza ce, Ayyukanta kuma na banza ne.

31 Don haka zan yi kuka saboda Mowab duka, Zan kuma yi baƙin ciki saboda mutanen Kir-heres.

32 Zan yi kuka saboda kurangar inabin Sibma Fiye da yadda zan yi kuka saboda mutanen Yazar. Rassanku sun haye teku har sun kai Yazar, Amma mai hallakarwa ya faɗo a kan 'ya'yan itatuwanku da damuna Da kan amfanin inabinku.

33 An ɗauke farin ciki da murna daga ƙasa mai albarka ta Mowab, Na hana ruwan inabi malala daga wurin matsewarsa, Ba wanda yake matse shi, yana ihu na murna, Ihun da ake yi ba na murna ba ne.

34 “Mutanen Heshbon da na Eleyale suna kururuwa ana iya jin kururuwansu a Yahaza. Ana iya jinta kuma a Zowar, da Horonayim, da Eglat-shelishiya. Har ma ruwan Nimra ya ƙafe.

35 Zan hana mutanen Mowab miƙa hadayu na ƙonawa a tuddai, da miƙa wa gumakansu sadaka, ni Ubangiji na faɗa.

36 “Zuciyata tana makoki domin Mowab da Kir-heres kamar wanda yake kukan makoki da sarewa saboda wadatarsu ta ƙare.

37 Gama kowa ya aske kansa da gemunsa, sun tsattsage hannuwansu. Kowa kuma ya sa rigar makoki.

38 Ba abin da ake yi a bisa kan soraye da dandali na Mowab sai baƙin ciki, gama na farfashe Mowab kamar tulun da ba a so, ni Ubangiji na faɗa.

39 An farfashe Mowab, ta yi kuka, ta kunyata! Ta zama abin dariya da abin tsoro ga waɗanda suke kewaye da ita.

40 “Ni Ubangiji na ce, Wani zai yi firiya da sauri kamar gaggafa, Zai shimfiɗa fikafikansa a kan Mowab.

41 Za a ci garuruwa da kagarai da yaƙi, A wannan rana zukatan sojojin Mowab Za su zama kamar zuciyar macen da take naƙuda.

42 Za a hallaka Mowab daga zaman al'umma, Domin ta tayar wa Ubangiji.

43 Tsoro, da rami, da tarko suna jiranku, Ya mazaunan Mowab, Ni Ubangiji na faɗa.

44 Wanda ya guje wa tsoro, Zai fāɗa a rami, Wanda kuma ya fito daga cikin rami, Tarko zai kama shi. Gama na sa wa Mowab lokacin da zan hukunta ta, Ni Ubangiji na faɗa.

45 “A ƙarƙashin inuwar Heshbon 'yan gudun hijira suna tsaye ba ƙarfi. Gama wuta ta ɓullo daga Heshbon, Harshen wuta kuma ya fito daga Sihon, Ta ƙone goshin Mowab da ƙoƙwan kai na 'yan tayarwa.

46 Kaitonku, ya Mowabawa! Mutanen Kemosh sun lalace, An kai 'ya'yanku mata da maza cikin bauta.

47 “Amma zan komar da mutanen Mowab nan gaba, Ni Ubangiji na faɗa.” Wannan shi ne hukuncin Mowab.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan