Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Irmiya 47 - Littafi Mai Tsarki


Jawabin Ubangiji a kan Filistiyawa

1 Kafin Fir'auna ya ci Gaza da yaƙi Ubangiji ya yi magana da Irmiya a kan Filistiyawa.

2 Ubangiji ya ce, “Ga shi, ruwa yana tasowa daga arewa, Zai zama kogi da yake ambaliya. Zai malala bisa ƙasa da dukan abin da yake cikinta, Da birni da mazauna cikinsa, Maza za su yi kuka, Dukan mazaunan ƙasar za su yi kuka.

3 Da jin takawar kofatan dawakai, Da amon karusai da ƙafafun karusai, Ubanni ba su juya, su dubi 'ya'yansu ba, Domin hannuwansu sun yi laƙwas,

4 Domin lokacin hallaka dukan Filistiyawa ya yi. Za a datse wa Taya da Sidon kowane taimakon da ya ragu, Gama Ubangiji zai hallaka Filistiyawa Waɗanda suke baƙin teku na Kaftor.

5 Baƙin ciki zalla ya sami Gaza, Ashkelon ta lalace. Ya ƙattin mutane, yaushe za ku daina tsattsage kanku?

6 Ya takobin Ubangiji, yaushe za ka huta? Sai ka koma ƙubenka, Ka huta, ka yi shiru!

7 Ƙaƙa zai huta, tun da ni Ubangiji ne na umarce shi? Ni Ubangiji na umarce shi ya yi yaƙi da Ashkelon Da mazauna a bakin teku.”

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan