Irmiya 45 - Littafi Mai TsarkiJawabin Irmiya ga Baruk 1 A shekara ta huɗu ta sarautar Yehoyakim, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, Baruk ɗan Neriya ya rubuta abin da Irmiya ya faɗa masa. 2 “Ubangiji Allah na Isra'ila ya ce maka, kai Baruk, 3 kai ka ce, ‘Kaitona, gama Ubangiji ya ƙara baƙin ciki a kan wahalaina, na gaji da nishina, ba ni da hutu!’ 4 “Sai ka faɗa wa Baruk cewa, ‘Ni Ubangiji na ce, ga shi, abin da na gina zan rushe shi, abin da kuma na dasa zan tumɓuke shi, wato ƙasar ɗungum. 5 Kana nemar wa kanka manyan abubuwa? Kada ka neme su, gama zan kawo masifa a kan dukan 'yan adam, amma zan kuɓutar da ranka kamar ganima, a dukan wuraren da za ka tafi.’ ” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria