Irmiya 31 - Littafi Mai Tsarki1 Ubangiji ya ce, “Lokaci yana zuwa da zan zama Allah na dukan iyalan Isra'ila, za su kuwa zama jama'ata.” 2 Haka Ubangiji ya ce, “Jama'ar da suka tsere wa takobi, Sun sami alheri a cikin jeji, A sa'ad da Isra'ila suka nemi hutawa.” 3-4 Ubangiji ya bayyana gare ni tun daga nesa cewa, “Ya Isra'ila, budurwa! Na kusace ki da madawwamiyar ƙaunata, Ba zan fasa amintacciyar ƙaunata a gare ki ba. Zan sāke gina ki, Za ki kuwa ginu, Za ki ɗauki kayan kaɗe-kaɗe, Za ki shiga rawar masu murna. 5 Za ki sāke dasa gonar inabi A kan duwatsun Samariya, Masu dashe za su dasa, Za su mori 'ya'yan. 6 Gama rana tana zuwa sa'ad da mai tsaro zai yi kira A ƙasar tudu ta Ifraimu, ya ce, ‘Ku tashi mu haura zuwa Sihiyona Zuwa wurin Ubangiji Allahnmu.’ ” 7 Ga abin da Ubangiji ya ce, “Raira wa Yakubu waƙar farin ciki da ƙarfi, Ku ta da murya saboda shugaban al'ummai, Ku yi shela, ku yi yabo, ku ce, ‘Ya Ubangiji ka ceci jama'arka, Wato ringin mutanen Isra'ila,’ 8 Ga shi, zan fito da su daga ƙasar arewa, Zan tattaro su daga manisantan wurare na duniya, Tare da su makafi da guragu, Da mace mai goyo da mai naƙuda, Za su komo nan a babbar ƙungiya. 9 Da kuka za su komo. Da ta'aziyya zan bishe su, in komar da su, Zan sa su yi tafiya a gefen rafuffukan ruwa, A kan miƙaƙƙiyar hanya, inda ba za su yi tuntuɓe ba. Gama ni uba ne ga Isra'ila, Ifraimu kuwa ɗan farina ne.” 10 “Ku ji maganar Ubangiji, Ya ku al'ummai, Ku yi shelarsa har a ƙasashen da suke nesa, na gāɓar teku. Ku ce, ‘Shi wanda ya warwatsa Isra'ila zai tattaro ta, Zai kiyaye ta kamar yadda makiyayi yakan kiyaye garkensa.’ 11 Gama Ubangiji ya fanshi Yakubu. Ya fanshe shi daga hannuwan waɗanda suka fi ƙarfinsa. 12 Za su zo su raira waƙa da ƙarfi, A bisa ƙwanƙolin Sihiyona, Za su yi annuri saboda alherin Ubangiji, Saboda hatsi, da ruwan inabi, da mai, Saboda 'ya'yan tumaki da na shanu. Rayuwarsu za ta zama kamar lambu, Ba za su ƙara yin yaushi ba. 13 Sa'an nan 'yan mata za su yi rawa da farin ciki, Samari da tsofaffi za su yi murna. Zan mai da makokinsu ya zama murna, Zan ta'azantar da su, in ba su farin ciki maimakon baƙin ciki. 14 Zan yi wa ran firistoci biki da wadata, Jama'ata za su ƙoshi da alherina, Ni Ubangiji na faɗa.” 15 Ga abin da Ubangiji ya ce, “An ji murya daga Rama, Muryar baƙin ciki da kuka mai zafi, Rahila tana kuka saboda 'ya'yanta, ba su. 16 Ki yi shiru, ki daina kuka, Ki shafe hawaye daga idanunki. Za a sāka miki wahalarki, Za su komo daga ƙasar abokin gāba, Ni Ubangiji na faɗa. 17 Akwai sa zuciya dominki a nan gaba, Ni Ubangiji na faɗa. 'Ya'yanki za su komo ƙasarsu. 18 “Na ji Ifraimu yana baƙin ciki, yana cewa, ‘Ka hore ni, na kuwa horu, Kamar ɗan maraƙin da ba shi da horo, Ka komo da ni don in zama kamar yadda nake a dā, Gama kai ne Ubangiji Allahna. 19 Gama na tuba saboda na rabu da kai, Bayan da aka ganar da ni, sai na sunkuyar da kai, Kunya ta kama ni, na gigice, Domin ina ɗauke da wulakancin ƙuruciyata.’ 20 Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa. 21 “Ki kafa wa kanki alamun hanya, Ki kafa wa kanki shaidu, Ki lura da gwadabe da kyau, Hanyar da kin bi, kin tafi. Ya budurwa Isra'ila, ki komo, Komo zuwa biranen nan naki. 22 Har yaushe za ki yi ta shakka, Ya ke 'yar marar bangaskiya? Gama Ubangiji ya halitta sabon abu a duniya, Mace ce za ta kāre namiji.” 23 Haka Ubangiji Mai Runduna, Allah na Isra'ila, ya ce, “Nan gaba za su sāke yin magana a ƙasar Yahuza da biranenta a sa'ad da na mayar musu da dukiyarsu. “ ‘Ubangiji ya sa maka albarka, Ya wurin zaman adalci, Ya tsattsarkan tudu!’ 24 Yahuza kuwa da dukan biranenta za su zauna tare a can, da manoma, da makiyaya, da garkunansu. 25 Gama zan biya bukatar waɗanda suka gaji, in wartsakar da waɗanda ransu ya yi yaushi.” 26 Irmiya ya farka, ya ce, “Ina kuwa cikin barcina mai daɗi sai na farka na duba.” Sabon Alkawari 27 “Ni Ubangiji na ce, ga shi, zan sa mutane da dabbobi su cika ƙasashen Isra'ila da na Yahuza. 28 Zai zama kamar yadda na lura da su don a tumɓuke su, a rushe su, a lalatar da su, a kawo musu masifa, haka kuma zan lura da su, a kuma dasa su, ni Ubangiji na faɗa. 29 A waɗannan kwanaki ba za su ƙara cewa, “ ‘Ubanni suka ci 'ya'yan inabi masu tsami, Haƙoran 'ya'ya suka mutu’ ba. 30 Amma kowa zai mutu saboda zunubin kansa, Wanda ya ci inabi masu tsami, Shi ne haƙoransa za su mutu.” 31 Ubangiji ya ce, “Ga shi, kwanaki suna zuwa da zan yi sabon alkawari da mutanen Isra'ila da na Yahuza. 32 Ba irin wanda na yi da kakanninsu ba, sa'ad da na fito da su daga ƙasar Masar, alkawarin da suka karya, ko da yake ni Ubangijinsu ne, ni Ubangiji na faɗa. 33 Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata. 34 Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.” 35 Haka Ubangiji ya ce, Shi wanda ya ba da rana ta haskaka yini, Ya sa wata da taurari su ba da haske da dare, Shi ne yakan dama teku, ya sa raƙumanta su yi ruri, Sunansa Ubangiji Mai Runduna. 36 “Idan dai wannan kafaffiyar ka'ida ta daina aiki a gabana, Ni Ubangiji na faɗa, To, ashe, zuriyar Isra'ila za ta daina zama al'umma a gabana ke nan har abada. 37 Idan a iya auna sammai a kuma iya bincike tushen duniya a ƙarƙas, To, ashe, zan watsar da dukan zuriyar Isra'ila ke nan saboda dukan abin da suka yi, Ni Ubangiji na faɗa. 38 “Ga shi, kwanaki suna zuwa da za a sāke gina birnin domin Ubangiji, ni Ubangiji na faɗa, tun daga hasumiyar Hananel zuwa yamma, har zuwa Ƙofar Kan Kusurwa. 39 Sa'an nan ma'aunin zai daɗa gaba, har ya kai tudun Gareb, sa'an nan ya nausa zuwa Gowa. 40 Dukan filin kwarin gawawwaki da toka, da dukan filaye har zuwa rafin Kidron zuwa kan kusurwar Ƙofar Doki wajen gabas, za su zama mai tsarki ga Ubangiji. Ba za a ƙara tumɓuke shi ko a rushe shi ba har abada.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria