Irmiya 3 - Littafi Mai Tsarki1 Ubangiji ya ce, “Idan mutum ya saki matarsa, Ta kuwa rabu da shi, har ta auri wani, Ya iya ya komo da ita? Ashe, yin haka ba zai ƙazantar da ƙasar ba? Ya Isra'ila, kin yi karuwanci, Abokan sha'anin karuwancinki, suna da yawa. Za ki sāke komowa wurina? Ni, Ubangiji, na faɗa. 2 Ki ta da idonki, ki duba filayen tuddai ki gani, Akwai wurin da ba ki laɓe kin yi karuwanci ba? Kin yi ta jiran abokan sha'anin karuwancinki a kan hanya, Kamar Balaraben da yake fako a hamada. Kin ƙazantar da ƙasar da mugun karuwancinki. 3 Saboda haka aka ƙi yin ruwa, Ruwan bazara bai samu ba. Goshinki irin na karuwa ne, ba ki jin kunya. 4 “Yanzu kin ce, ‘Kai ne mahaifina, Ka ƙaunace ni tun ina cikin ƙuruciyata. 5 Za ka dinga yin fushi da ni? Za ka husata da ni har abada?’ Ga shi, ke kika faɗa, amma ga shi, kin aikata dukan muguntar da kika iya yi.” Dole Isra'ila da Yahuza su Tuba 6 A zamanin sarki Yosiya, Ubangiji ya ce mini, “Ka ga abin da take yi, ita marar amincin nan, wato Isra'ila? Yadda a kowane tudu mai tsayi, da a gindin kowane itace mai duhuwa, a wurare ne ta yi karuwancinta. 7 Na yi zaton bayan da ta aikata wannan duka, za ta komo wurina. Amma ba ta komo ba, maƙaryaciyar 'yar'uwarta, wato Yahuza, ta gani. 8 Yahuza kuwa ta ga dukan karuwancin da marar amincin nan, Isra'ila ta yi, na sake ta, na ba ta takardar sarki. Amma duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza, ba ta ji tsoro ba, amma ita ma ta tafi ta yi karuwanci. 9 Domin karuwanci a wurinta abu ne mai sauƙi, ta ƙazantar da ƙasar. Ta yi karuwanci da duwatsu, da itatuwa. 10 Duk da haka maƙaryaciyar 'yar'uwan nan tata, Yahuza ba ta juyo wurina da zuciya ɗaya ba, sai a munafunce, ni Ubangiji na faɗa.” 11 Ubangiji kuma ya faɗa mini, ko da yake Isra'ila ta bar binsa, duk da haka ta nuna laifinta bai kai na Yahuza marar aminci ba. 12 Ya ce mini in tafi wajen arewa in yi shela in ce, “Ki komo ya Isra'ila, marar aminci, Ni Ubangiji, na faɗa. Domin ni mai jinƙai ne, Ba zan yi fushi da ke ba. Ba zan yi fushi da ke har abada ba, Ni, Ubangiji na faɗa. 13 Ke dai ki yarda da laifinki, Da kika yi wa Ubangiji Allahnki, Kin kuma watsar da mutuncinki a wurin baƙi A gindin kowane itace mai duhuwa. Kika ƙi yin biyayya da maganata, Ni, Ubangiji, na faɗa. 14 “Ku komo, ya ku mutane marasa aminci, Gama ni ne Ubangijinku. Zan ɗauki mutum guda daga kowane gari, In ɗauki mutum biyu daga kowane iyali, Zan komo da su zuwa Dutsen Sihiyona. 15 Zan ba ku sarakuna waɗanda suke yi mini biyayya da hikima da fahimi. 16 Sa'ad da kuka yawaita a ƙasar, mutane ba za su ƙara yin magana a kan akwatin alkawari na Ubangiji ba. Ba za su ƙara yin tunaninsa ko su tuna da shi, ko su bukace shi, ko kuwa su yi wani irinsa ba. 17 In lokacin nan ya yi, za a kira Urushalima gadon sarautar Ubangiji, dukan sauran a'umma za su taru a Urushalima da sunana. Ba za su ƙara bin tattaurar zuciyarsu mai mugunta ba. 18 A waɗannan kwanaki mutanen Yahuza za su haɗu da mutanen Isra'ila. Tare za su zo daga ƙasar arewa zuwa cikin ƙasar da na ba kakanninku gādo.” 19 “Isra'ila, na yi niyya in karɓe ku kamar ɗana, In gādar muku da kyakkyawar ƙasa Mafi kyau a dukan duniya. Na zaci za ku ce ni ne mahaifinku, Ba za ku ƙara rabuwa da bina ba. 20 Hakika kamar yadda mace marar aminci takan bar mijinta, Haka kun zama marar aminci a gare ni, ya jama'ar Isra'ila. Ni Ubangiji, na faɗa.” 21 An ji murya a kan filayen tuddai, Kūka da roƙo ne na 'ya'yan Isra'ila maza, Domin sun rabu da hanyarsu, Sun manta da Ubangiji Allahnsu. 22 “Ku juyo ku marasa aminci, Zan warkar da rashin amincinku. “To, ga shi, mun zo gare ka, Gama kai ne Ubangiji Allahnmu, 23 Daga kan tuddai ba mu da wani taimako, Ko daga hayaniyar da ake yi a kan duwatsu, Daga wurin Ubangiji Allahnmu ne kaɗai taimakon Isra'ila yake fitowa. 24 “Amma yin sujada ga gunkin nan Ba'al ya cinye mana amfanin wahalar da kakanninmu suka sha tun muna yara, wato na garkunan tumakinsu, da na awakinsu, da na shanunsu, da 'ya'yansu mata da maza. 25 Bari mu kwanta mu sha kunyarmu, bari kuma rashin kirkinmu ya rufe mu. Gama mun yi wa Ubangiji Allahnmu zunubi mu da kakanninmu, tun daga ƙuruciyarmu har zuwa yau, ba mu yi biyayya ga maganar Ubangiji Allahnmu ba.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria