Irmiya 2 - Littafi Mai TsarkiUbangiji Ya Ji da Isra'ila da Masu Ridda 1 Ubangiji ya ce mini, 2 in tafi in yi shelar abin da Ubangiji ya ce a kunnen Urushalima, in ce, “Na tuna da amincinki a lokacin ƙuruciyarki, Da ƙaunarki kamar ta amarya da ango. Yadda kika bi ni a cikin jeji, da a ƙasar da ba a shuka ba. 3 Isra'ila tsattsarka ce ta Ubangiji, Nunar fari ta girbina. Dukan waɗanda suka ci daga cikinki sun yi laifi, Masifa za ta auko miki. Ni Ubangiji, na faɗa.” 4 Ku ji jawabin Ubangiji, ku zuriyar Yakubu, ku dukan kabilan Isra'ila. 5 Ubangiji ya ce, “Wane laifi ne na yi wa kakanninku, Da suka bar bina? Suka bauta wa gumaka marasa amfani, Su kuma suka zama marasa amfani. 6 Ba su kula da ni ba, Ko da yake na cece su daga ƙasar Masar. Na bi da su a cikin hamada, A ƙasa mai tuddai da kwazazzabai, Busasshiya mai yawan hatsari, Ba a bi ta cikinta, Ba wanda yake zama cikinta kuma. 7 Na kawo su zuwa ƙasa mai dausayi, Don su more ta su ci amfaninta, Amma da suka shiga, sun ƙazantar mini da ita, Suka sa ƙasar da na gādar musu ta zama abar ƙyama. 8 Firistoci kuma ba su ce, ‘Ina Ubangiji Yake’ ba? Masanan shari'a ba su san ni ba. Masu mulki sun yi mini laifi, Annabawa sun yi annabci da sunan Ba'al, Sun bi waɗansu abubuwa marasa amfani.” Shari'ar da Ubangiji yake Yi wa Mutanensa 9 “Domin haka, ni Ubangiji zan gabatar da ku gaban shari'a. Ku da 'ya'yanku, da 'ya'yan 'ya'yanku, wato jikokinku. 10 Ku haye zuwa tsibirin Kittim wajen yamma, ku gani, Ku aika zuwa Kedar wajen gabas, ku duba da kyau, A dā an taɓa yin wani abu haka? 11 Akwai wata al'umma da ta taɓa sāke gumakanta Ko da yake su ba kome ba ne? Amma mutanena sun sauya darajarsu da abin da ba shi da rai. 12 Sammai, ku girgiza saboda wannan, ku razana, Ku yi shiru, ni Ubangiji na faɗa. 13 Mutanena sun yi zunubi iri biyu, Sun rabu da ni, ni da nake maɓuɓɓugar ruwan rai, Sun haƙa wa kansu tafkunan ruwa, hudaddu, Waɗanda ba za su iya ajiye ruwa ba. 14 “Isra'ila ba bawa ba ne, ba a kuma haife shi bawa ba, Amma me ya sa ya zama ganima? 15 Zakuna suna ruri a kansa, Suna ruri da babbar murya. Sun lalatar da ƙasarsa, Garuruwansa sun lalace, Ba wanda yake zaune cikinsu. 16 Mutanen Memfis kuma da na Tafanes sun fasa ƙoƙwan kansa. 17 Ya Isra'ila, kai ne ka jawo wa kanka wannan, Da ka rabu da Ubangiji Allahnka, Sa'ad da ya bishe ka a hanya. 18 Wace riba ka samu, har da ka tafi Masar, Don ka sha ruwan Kogin Nilu? Wace riba ka samu, har da ka tafi Assuriya, Don ka sha ruwan Kogin Yufiretis? 19 Muguntarka za ta hore ka, Riddarka kuma za ta hukunta ka. Sa'an nan za ka sani, ka kuma gane, Ashe, mugun abu ne, mai ɗaci, a gare ka Ka rabu da Ubangiji Allahnka, Ba ka tsorona a zuciyarka. Ni Ubangiji, Allah Mai Runduna na faɗa.” Isra'ila Ya Ƙi Yi wa Ubangiji Biyayya 20 “Ya Isra'ila, tun da daɗewa, ka ƙi yarda Ubangiji ya mallake ka, Ka ƙi yin biyayya da ni, Ka kuwa ce, ‘Ba zan yi bauta ba.’ Amma ka yi karuwanci a kan kowane tudu, Da kowane ɗanyen itace. 21 Na dasa ka kamar zaɓaɓɓiyar kurangar inabi, zaɓaɓɓen iri mafi kyau. Ta yaya ka lalace haka ka zama rassan kurangar inabi ta jeji, Waɗanda ba zan yarda da su ba? 22 Ko da za ka yi wanka da sabulun salo, Ka yi amfani da sabulu mai yawa, Duk da haka zan ga tabban zunubanka. Ni Ubangiji Allah na faɗa. 23 Ƙaƙa za ka ce ba ka ƙazantar da kanka ba, Ba ka taɓa bin gunkin nan Ba'al ba? Ka duba hanyarka ta zuwa cikin kwari, ka san abin da ka yi. Kana kama da taguwa, mai yawon neman barbara. 24 Kamar jakar jeji kake, wadda take son barbara, Wadda take busar iska, Sa'ad da take son barbara, wa zai iya hana ta? Jakin da take sonta, ba ya bukatar wahalar da kansa Gama a watan barbararta za a same ta. 25 Kai Isra'ila, kada ka bar ƙafafunka ba takalma, Kada kuma ka bar maƙogwaronka ya bushe. Amma ka ce, ‘Wannan ba amfani, Gama na ƙaunaci baƙi, su kuwa zan bi.’ 26 “Kamar yadda ɓarawo yakan sha kunya sa'ad da aka kama shi, Haka nan mutanen Isra'ila za su sha kunya, Da su, da sarakunansu, da shugabanninsu, Da firistocinsu, da annabawansu. 27 Waɗanda suka ce wa itace, ‘Kai ne mahaifinmu.’ Suna kuma ce wa dutse, ‘Kai, ka haife mu.’ Gama sun ba ni baya, ba su fuskance ni ba. Amma sa'ad da suke shan wahala, sukan ce, ‘Ka zo ka taimake mu.’ 28 Ina gumakan da kuka yi wa kanku? Bari su tashi in sun iya cetonku lokacin wahalarku. Yahuza, yawan gumakanku sun kai Yawan garuruwanku. 29 Ni Ubangiji, ina tambayarku, ‘Wace ƙara kuke da ita game da ni?’ Kun yi mini tawaye dukanku. 30 Na hori 'ya'yanku, amma a banza, ba su horu ba, Kun kashe annabawanku da takobi kamar mayunwacin zaki. 31 Ya ku mutanen zamanin nan, ku saurari maganata. Na zamar wa Isra'ila jeji? Ko ƙasar da take da kurama? Don me fa mutanena suke cewa, ‘Mu 'yantattu ne, Ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’? 32 Budurwa ta manta da kayan kwalliyarta? Ko kuwa amarya ta manta da kayan adonta? Amma mutanena sun manta da ni kwanaki ba iyaka. 33 Kun sani sarai yadda za ku yi ku farauci masoya, Har mugayen mata ma, kun koya musu hanyoyinku. 34 Tufafinku sun ƙasantu da jinin marasa laifi, Waɗanda ba ku same su suna fasa gidajenku ba. Amma duk da haka kuna cewa, 35 ‘Ba mu da laifi, hakika kuwa, Ubangiji bai yi fushi da mu ba.’ Amma ni Ubangiji zan hukunta ku, Domin kun ce ba ku yi zunubi ba. 36 Me ya sa ba ku da tsayayyiyar zuciya, Sai ku yi nan ku yi can? Masar za ta kunyata ku kamar yadda Assuriya ta yi. 37 Da hannuwanku a kā za ku komo daga Masar don kunya. Gama waɗanda kuke dogara gare su, ni Ubangiji, na ƙi su, Ba za ku yi arziki tare da su ba.” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria