Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Irmiya 10 - Littafi Mai Tsarki


Gumaka da Allah na Gaskiya

1 Ya jama'ar Isra'ila, ku ji jawabin da Ubangiji yake yi muku.

2 Ubangiji ya ce, “Kada ku koyi abubuwan da al'ummai suke yi, Kada ku ji tsoron alamun da suke a sama, Ko da yake al'ummai suna jin tsoronsu.

3 Gama al'adun mutane na ƙarya ne, Daga cikin jeji aka sare wani itace, Gwanin sassaƙa ya sassaƙa shi da gizago.

4 Mutane sukan yi masa ado na azurfa da zinariya, Sukan ɗauki guduma su kafa shi da ƙusoshi, Don kada ya motsa.

5 Gumakansu dodon gona suke, a cikin gonar kabewa, Ba su iya yin magana, Ɗaukarsu ake yi domin ba su iya tafiya! Kada ku ji tsoronsu. Gama ba su da ikon aikata mugunta ko alheri.”

6 Ya Ubangiji, ba wani kamarka, Kai mai girma ne, Sunanka kuma yana da girma da iko.

7 Wane ne ba zai ji tsoronka ba, ya Sarkin dukan al'ummai? Ka isa a ji tsoronka, Gama babu kamarka a cikin dukan masu hikima na al'ummai, Da kuma cikin dukan mulkokinsu, Ba wani kamarka.

8 Dukansu dakikai ne wawaye, Koyarwar gumaka ba wani abu ba ne, itace ne kawai!

9 An kawo fallayen azurfa daga Tarshish, Da zinariya kuma daga Ufaz, Aikin gwanaye da maƙeran zinariya. Tufafinsu na mulufi ne da shunayya, duka aikin gwanaye.

10 Amma Ubangiji shi ne Allah na gaskiya, Shi Allah mai rai ne, Shi Sarki ne madawwami. Saboda hasalarsa duniya ta girgiza, Al'ummai ba za su iya jurewa da fushinsa ba.

11 Haka za ku faɗa musu, “Gumakan da ba su yi sammai da duniya ba, za su lalace a duniya da a ƙarƙashin sammai.”

12 Shi ne, ta wurin ikonsa ya yi duniya, Ta wurin hikimarsa ya kafa ta, Ta wurin basirarsa kumaya ya shimfiɗa sammai.

13 Sa'ad da ya yi murya akan ji ƙugin ruwa a cikin sammai Yakan kawo ƙasashi daga ƙurewar duniya, Yakan yi walƙiyoyi saboda ruwan sama, Daga cikin taskokinsa yakan kawo iska.

14 Kowane mutum dakiki ne, marar ilimi, Kowane maƙerin zinariya zai sha kunya saboda gumakansa, Gama siffofinsa ƙarya ne, Ba numfashi a cikinsu.

15 Su ba kome ba ne, aikin ruɗami ne, A lokacin da za a hukunta su za su lalace.

16 Gama shi ba kamar waɗannan yake ba, Shi na Yakubu ne. Shi ne ya yi dukan kome, Kabilan Isra'ilawa gādonsa, Sunansa Ubangiji Mai Runduna.


Risɓewar Yahuza

17 Ku tattara kayayyakinku, Ku mazaunan wurin da aka kewaye da yaƙi.

18 Gama haka Ubangiji ya ce, “Ga shi, ina jefar da mazaunan ƙasar daga ƙasarsu a wannan lokaci, Zan kawo musu wahala, za su kuwa ji jiki.”

19 Tawa ta ƙare, saboda raunin da aka yi mini. Raunina mai tsanani ne, Amma na ce, lalle wannan azaba ce, Tilas in daure da ita.

20 An lalatar da alfarwata, Dukan igiyoyi sun tsintsinke, 'Ya'yana maza sun bar ni, ba su nan. Ba wanda zai kafa mini alfarwata Ya kuma rataya labulena.

21 Makiyayan dakikai ne, Ba su roƙi Ubangiji ba, Don haka ba su sami wadata ba, An watsa dukan garkensu.

22 Ku ji fa, an ji ƙishin-ƙishin! Ga shi kuma, yana tafe. Akwai babban hargitsin da ya fito daga arewa, Don a mai da biranen Yahuza kufai, wurin zaman diloli.

23 “Ya Ubangiji, na sani al'amuran mutum ba a hannunsa suke ba, Ba mutum ne yake kiyaye takawarsa ba

24 Ka tsauta mini, ya Ubangiji, amma da adalcinka, Ba da fushinka ba, don kada ka wofinta ni.

25 Ka kwarara hasalarka a kan sauran al'umma da ba su san ka ba, Da a kan jama'ar da ba su kiran sunanka, Gama sun cinye Yakubu, Sun cinye shi, sun haɗiye shi, Sun kuma mai da wurin zamansa kufai.”

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan