Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ibraniyawa 9 - Littafi Mai Tsarki


Wurare Tsarkaka na Duniya da na Sama

1 Alkawarin farko yana da ka'idodinsa na yin sujada, da kuma wurin yinta tsattsarka wanda mutane suka shirya.

2 Wato, an kafa alfarwa wadda sashinta na farko yake da fitila, da tebur, da kuma keɓaɓɓiyar gurasa. Ana kiran wannan sashi Wuri Mai Tsarki.

3 Bayan labule na biyu kuma, akwai sashin alfarwa da ake kira Wuri Mafi Tsarki.

4 A cikinsa kuwa da faranti na zinariya domin ƙona turare, da kuma akwatin alkawari da aka yi masa laffa da zinariya ta kowane gefe. A cikinsa kuwa akwai tasar zinariya da manna a ciki, da sandar Haruna wadda ta yi toho, da kuma allunan dutse na alkawarin nan.

5 A bisa akwatin alkawari kuma akwai kerubobin nan na ɗaukakar Allah, waɗanda suka yi wa murfin akwatin nan laima. Ba za mu iya yin maganar waɗannan abubuwa filla filla ba a yanzu.

6 In an gama waɗannan shirye-shirye haka, sai firistoci kullum su riƙa shiga sashin farko an alfarwar, suna hidimarsu ta ibada.

7 Amma na biyun, sai babban firist kaɗai yake shiga, shi ma kuwa sai sau ɗaya a shekara, sai kuma da jini wanda yakan miƙa saboda kansa, da kuma kurakuran jama'a.

8 Ta haka Ruhu Mai Tsarki yake yin ishara, cewa ba a buɗe hanyar shiga Wuri Mafi Tsarki ba tukuna, muddin alfarwa tana nan a tsaye,

9 wadda take ishara ce ga wannan zamani. Bisa ga wannan ishara akan yi miƙa sadaka da hadaya, amma ba sa iya kammala lamirin mai ibadar,

10 tun da yake ci da sha da wankewanke iri iri kaɗai suke shafa, ka'idodi ne a game da jiki kurum, waɗanda aka sa kafin a daidaita al'amari.

11 Amma Almasihu ya riga ya zo, yana babban firist na kyawawan abubuwan da suke akwai. Masujadar da yake hidima a ciki mafi ɗaukaka ce, mafi kammala kuwa (wadda ba yin mutum ba ce, wato, ba ta wannan halittacciyar duniya ba ce).

12 Almasihu ya shiga Wuri Mafi Tsarki sau ɗaya tak, ba ƙari, ba kuwa ta wurin jinin awaki ko na 'yan maruƙa ya shiga ba, sai dai ta wurin nasa jini, ya samo mana madawwamiyar fansa.

13 To, jinin awaki ne fa da na bijimai, da kuma tokar karsana da ake yayyafa wa waɗanda suka ƙazantu, suke tsarkake su da tsabtacewar jiki,

14 balle fa jinin Almasihu wanda ya miƙa kansa marar aibu ga Allah, ta wurin Madawwamin Ruhu, lalle zai tsarkake lamirinmu daga barin ibada marar tasiri, domin mu bauta wa Allah Rayayye.

15 Saboda haka, shi ne matsakancin sabon alkawari, domin waɗanda aka kira su karɓi dawwamammen gādon da aka yi musu alkawari, tun da yake an yi wata mutuwa mai fansar waɗanda suke keta umarni a game da alkawarin farko.

16 A game da al'amarin wasiyya, lalle ne a tabbatar da mutuwar wanda ya yi ta tukuna.

17 Domin ba a zartar da wasiyya sai bayan an mutu, tun da yake ba a yin aiki da ita muddin wanda ya yi ta yana a raye.

18 Ashe kuwa, mun ga alkawarin nan na farko, ba a tabbatar da shi ba, sai a game da jini.

19 Don bayan Musa ya sanar da kowane umarnin Shari'a ga dukan jama'a, sai ya ɗebi jinin 'yan maruƙa da na awaki, tare da ruwa, da jan ulu, da kuma ganyen izob, ya yayyafa wa Littafin kansa, da kuma duk jama'a,

20 yana cewa, “Wannan shi ne jini na tabbatar alkawarin nan, da Allah ya yi umarni a game da ku.”

21 Haka kuma, ya yayyafa jinin ga alfarwar nan, da dukan kayanta na yin hidima.

22 Hakika, bisa ga Shari'a, kusan kowane abu da jini ake tsarkake shi, in ba a game da zubar da jini ba kuwa, to, ba gafara.


Almasihu ya Miƙa Kansa domin Kawar da Zunubi

23 Da waɗannan abubuwa ne, ya wajaba a tsarkake makamantan abubuwan da suke a Sama, sai dai ainihin abubuwan Sama za a tsarkake su ne da hadayar da ta fi waɗannan kyau.

24 Domin Almasihu bai shiga wani wuri tsattsarka da mutum ya yi ba, wanda yake sura ne kawai na gaskataccen, a'a Sama kanta ya shiga, domin yă bayyana a gaban zatin Allah a yanzu saboda mu.

25 Ba kuwa domin ya riƙa miƙa kansa hadaya a kai a kai ba ne, kamar yadda babban firist yake shiga Wuri Mafi Tsarki a kowace shekara da jinin da ba nasa ba ne.

26 In da haka ne, ashe, da sai lalle ya yi ta shan wuya a kai a kai ke nan, tun daga farkon duniya. Amma a yanzu ya bayyana sau ɗaya tak, a ƙarshen zamanai, domin ya kawar da zunubi ta wurin miƙa kansa hadaya.

27 Tun da yake an ƙaddara wa ɗan adam ya mutu sau ɗaya ne, bayan haka kuma sai shari'a,

28 shi Almasihu ma, da aka miƙa shi hadaya sau ɗaya tak, domin ya ɗauke zunuban mutane da yawa, zai sāke bayyana, bayyana ta biyu, ba a kan maganar kawar da zunubi ba, sai dai domin yă ceci waɗanda suke ɗokin zuwansa.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan