Ibraniyawa 8 - Littafi Mai TsarkiBabban Firist na Sabon Alkawari 1 Wato, duk manufar maganarmu ita ce wannan. Shi ne irin babban firist wanda muke da shi, wato wanda ya zauna a dama da kursiyin Maɗaukaki a can sammai, 2 mai hidima a Wuri Mafi Tsarki, da kuma masujada ta gaskiya, wadda Ubangiji ya kafa, ba mutum ba. 3 Kowane babban firist akan sa shi domin ya miƙa sadakoki da hadayu, saboda haka wajibi ne wannan shi ma, ya zamanto yana da abin da zai miƙa. 4 To, ashe, da har yanzu yana duniya, da bai zama firist ba ke nan, tun da yake akwai firistocin da suke miƙa sadakoki bisa ga Shari'a. 5 Suna bauta wa makamantan abubuwan Sama da kuma ishararsu, kamar yadda Allah ya gargaɗi Musa sa'ad da yake shirin kafa alfarwar nan, da ya ce, “Ka lura fa, ka shirya kome da kome daidai yadda aka nuna maka a kan dutsen.” 6 Amma ga ainihi, Almasihu ya sami hidima wadda take mafificiya, kamar yadda alkawarin nan, wanda shi ne matsakancinsa, yake da fifiko nesa, tun da yake an kafa shi ne a kan mafifitan alkawarai. 7 Domin da wancan alkawari na farko bai gaza da kome ba, da ba sai an sāke neman na biyu ba. 8 Gama ya ga laifinsu da ya ce, “Lokaci yana zuwa, in ji Ubangiji, Da zan tsara sabon alkawari da jama'ar Isra'ila, Da kuma zuriyar Yahuza. 9 Ba irin alkawarin da na yi da kakanninsu ba, A ranar da na kama hannunsu Domin in fito da su daga ƙasar Masar. Saboda ba su tsaya ga alkawarina ba, Shi ya sa na ƙyale su, in ji Ubangiji. 10 Wannan shi ne alkawarin da zan yi da jama'ar Isra'ila, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Wato, zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu. Zan kasance Allahnsu, Su kuma su kasance jama'ata. 11 Ba kuma sai sun koya wa ɗan garinsu ba, Balle wani ya ce ɗan'uwansa, ‘Kă san Ubangiji!’ Domin kowa zai san ni, Daga ƙaraminsu, har ya zuwa babbansu. 12 Domin zan yi musu jinƙai a kan muguntarsu, Ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.” 13 Da ya ce sabon alkawari, ashe kuwa, ya mai da na farkon tsoho ke nan. Abin da yake tsufa, yana kuwa daɗa tsofewa, lalle ya yi kusan shuɗewa ke nan. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria