Ibraniyawa 6 - Littafi Mai Tsarki1 Saboda haka, sai mu ci gaba a kan ka'idodin farko na al'amarin Almasihu, har ya zuwa kammala, ba wai mu sāke koyar da jigajigan nan na tuba da ibada marar tasiri ba, da na gaskatawa da Allah, 2 da kuma na koyarwa a kan wanke-wanke, da ɗora hannu, da tashin matattu, da dawwamammen hukunci. 3 Za mu kuwa ci gaba in Allah ya yarda. 4 Domin waɗanda aka haskaka zukatansu sarai, har suka ɗanɗana baiwar nan ta Basamaniya, suka kuma sami rabo na ruhu mai tsarki, 5 har suka ɗanɗana daɗin Maganar Allah, da ikon zamani mai zuwa, 6 sa'an nan kuma suka ridda, ba mai yiwuwa ba ne a sāke jawo su ga tuba, tun da yake sāke gicciye Ɗan Allah suke yi, su da kansu, suka kuma wulakanta shi a sarari. 7 Ƙasa ma da take shanye ruwan da ake yi mata a kai a kai, take kuma fid da tsire-tsire masu amfani ga waɗanda ake noma ta dominsu, Allah yakan sa mata albarka. 8 Amma tsire-tsirenta ƙaya ne da kashin yawo, ba ta da amfani ke nan, tana kuma gab da la'antarwa, ƙarshenta dai ƙonewa ne. Tabbataccen Bege 9 Ko da yake mun faɗi haka, a game da ku kam, ya ƙaunatattu, mun tabbata kuna a kan abubuwa mafiya kyau na zancen ceto. 10 Gama Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi, wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi. 11 Muna dai bukata ƙwarai kowannenku ya nuna irin wannan himma ga yin cikkaken bege, tabbatacce, har ya zuwa ƙarshe, 12 don kada ku yi ragwanci, sai dai ku yi koyi da waɗanda suka karɓi cikar alkawaran nan, ta wurin bangaskiyarsu da haƙurinsu. 13 Sa'ad da Allah ya yi wa Ibrahim alkawari, da yake ba wani wanda ya fi shi girma da zai rantse da shi, sai ya rantse da kansa, 14 ya ce, “Hakika zan yi maka albarka, in kuma riɓanya zuriyarka.” 15 Ta haka Ibrahim, bayan da ya jure da haƙuri, ya karɓi cikar alkawarin. 16 Hakika mutane sukan rantse da abin da ya fi su, rantsuwa kuma ita ce abar da take tabbatarwa a duk lokacin gardama. 17 Don haka, sa'ad da Allah yake son ƙara tabbatar wa magādan alkawarin nan dahir, cewa nufinsa ba mai sākewa ba ne sam, sai ya haɗa da rantsuwa, 18 domin albarkacin abubuwa guda biyun nan marasa sākewa, masu nuna, cewa ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya, mu da muka gudu muka sami mafaka, mu ƙarfafa ƙwarai mu riski abin da muka kafa bege a kai. 19 Begen nan kuwa da muke da shi, kamar anka yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen, 20 a inda saboda mu ne Yesu ya riga mu shiga, da yake ya zama Babban Firist na har abada, kwatancin ɗabi'ar Malkisadik. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria