Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ibraniyawa 5 - Littafi Mai Tsarki

1 Kowane babban firist, da yake an zaɓe shi ne daga cikin mutane, akan sa shi yă wakilci mutane ga al'amarin Allah, don yă miƙa sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai.

2 Yă kuma zamana wanda zai iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da yake rarrauna ne shi ta ko'ina.

3 Saboda haka, wajibi ne yă miƙa hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama'a kaɗai ba, har ma don nasa.

4 Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna.

5 Haka kuma, Almasihu, ba shi ya ɗaukaka kansa ya zama Babban Firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi, “Kai Ɗana ne, Ni Ubanka ne yau.”

6 Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce, “Kai firist ne na har abada, Kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.”

7 Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.

8 Ko da yake shi Ɗa ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha,

9 da ya kai ga kammala, sai ya zama tushen madawwamin ceto ga dukkan waɗanda suke masa biyayya,

10 gama Allah yana kiransa Babban Firist, kwatancin ɗabi'ar Malkisadik.


Faɗakarwa a kan Wata Koyarwa Dabam

11 Muna da abu da yawa da za mu faɗa a game da shi kuwa, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe.

12 Ko da yake kamar a yanzu kam, ai, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sāke koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba, har ya zamana sai an ba ku nono, ba abinci mai tauri ba.

13 Ai, duk wanda yake nono ne abincinsa, bai ƙware da maganar adalci ba, kamar jariri yake.

14 Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato waɗanda hankalinsu ya horu yau da kullum, su rarrabe nagarta da mugunta.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan