Ibraniyawa 4 - Littafi Mai Tsarki1 Saboda haka tun alkawarin shiga inuwarsa tana nan, sai mu yi tsananin kula, kada ya zamana waninku ya kāsa shiga. 2 Ai kuwa, an yi mana albishir kamar yadda aka yi musu, sai dai maganar da aka yi musu ba ta amfane su da kome ba, don kuwa ba ta gamu da bangaskiya ga majiyanta ba. 3 Mu kuwa da muka ba da gaskiya, muna shiga inuwar, yadda ya ce, “Sai na yi rantsuwa da fushina, na ce, ‘ba za su shiga inuwata ba sam,’ ” ko da yake ayyukan Allah gamammu ne tun daga farkon duniya. 4 Domin a wani wuri ya yi maganar rana ta bakwai cewa, “A rana ta bakwai Allah ya huta daga ayyukansa duka.” 5 Amma a wannan wuri kuwa sai ya ce, “Ba za su shiga inuwata ba sam.” 6 Wato, tun da yake har yanzu dai da sauran dama waɗansu su shiga, su kuwa waɗanda aka fara yi wa albishirin nan sun kāsa shiga saboda rashin biyayya, 7 to, sai ya sāke sa wata rana, ya ce, “Yau,” yana magana ta bakin Dawuda bayan da aka daɗe, kamar an riga an faɗa cewa, “Yau in kun ji muryarsa, kada ku taurare zukatanku.” 8 Da dai a ce Joshuwa ya kai su cikin inuwar Allah, da Allah bai yi maganar wata rana nan gaba ba, 9 wato, har yanzu dai akwai sauran wani hutun Asabar ga jama'ar Allah, 10 domin kuwa duk wanda ya shiga inuwar Allah, ya huta ke nan daga ayyukansa, kamar yadda Allah yă huta daga nasa. 11 Saboda haka, sai mu yi himmar shiga inuwar nan, kada wani yă kāsa shiga, saboda irin wannan rashin biyayya. 12 Domin Maganar Allah rayayyiya ce, mai ƙarfin aiki, ta fi kowane irin takobi kaifi, har tana ratsa rai da ruhu, da kuma gaɓoɓi, har ya zuwa cikin ɓargo, tana kuma iya rarrabe tunanin zuciya da manufarta. 13 Ba wata halittar da za ta iya ɓuyar masa, amma kowane abu a fili yake, a shanye sosai a gaban idon wannan da za mu ba da lissafi a gabansa. Yesu Babban Firist Mai Girma 14 To, tun da yake muna da Babban Firist mai girma, wanda ya ratsa sammai, wato Yesu Ɗan Allah, sai mu tsaya a kan abin da muka bayyana yarda a gare shi. 15 Gama Babban Firist da muke da shi ba marar juyayin kasawarmu ba ne, a'a, shi ne wanda aka jarabce shi ta kowace hanya da aka jarabce mu, amma bai yi zunubi ba. 16 Saboda haka, sai mu kusaci kursiyin Allah na alheri da amincewa, domin a yi mana jinƙai, a kuma yi mana alherin da zai taimake mu a kan kari. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria