Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ibraniyawa 3 - Littafi Mai Tsarki


Fifikon Almasihu a kan Musa

1 Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa,

2 shi da yake mai aminci ga wannan da ya sa shi, kamar yadda Musa ya yi ga duk jama'ar Allah.

3 Amma kuwa an ga Yesu ya cancanci ɗaukaka fiye da ta Musa nesa, kamar yadda mai gina gida ya fi gidan martaba.

4 Kowane gida ai, da wanda ya gina shi, amma maginin dukkan abubuwa Allah ne.

5 To, shi Musa mai aminci ne ga dukkan jama'ar Allah a kan shi bara ne, saboda shaida a kan al'amuran da za a yi maganarsu a nan gaba,

6 amma Almasihu mai aminci ne, yana mulkin jama'ar Allah a kan shi Ɗa ne, mu ne kuwa jama'arsa, muddin mun tsaya gabanmu gaɗi, muna gadara da begenmu ƙwarai.


Shiga Inuwar Allah, Hutawar Mutanensa ke Nan

7 Saboda haka, kamar yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau in kun ji muryarsa,

8 Kada ku taurare zukatanku kamar a lokacin tawayen nan, Wato, ranar gwaji a jeji,

9 A inda kakanninku suka gwada ni, suka jarraba ni, Suna ganin ayyukana har shekara arba'in.

10 Saboda haka ne, na yi fushi da mutanen wannan zamani, Har na ce, ‘A kullum zuciyarsu a karkace take, Ba su kuwa san hanyoyina ba.’

11 Sai na yi rantsuwa da fushina, na ce, ‘Ba za su shiga inuwata ba sam.’ ”

12 Ku kula fa, 'yan'uwa, kada wata muguwar zuciyar marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye.

13 Sai dai kowace rana ku ƙarfafa wa juna zuciya muddin akwai “Yau”, don kada kowannenku ya taurare, ta yaudarar zunubi.

14 Don kuwa mun zama masu tarayya da Almasihu, muddin muna tsaye da ƙarfi a kan amincewar nan tamu ta fari, har zuwa ƙarshe.

15 Domin kuwa an ce, “Yau in kun ji muryarsa, Kada ku taurare zukatanku kamar a lokacin tawayen nan.”

16 To, su wane ne suka ji, duk da haka suka yi tawaye? Ashe, ba duk waɗanda suka fito daga ƙasar Masar ba ne, waɗanda Musa ya shugabantar?

17 Da su wa kuma ya yi fushi har shekara arba'in? Ashe, ba da waɗanda suka yi zunubi ba ne, waɗanda gawawwakinsu suka fādi a jeji?

18 Su wa kuma ya rantse wa, cewa ba za su shiga inuwarsa ba, in ba marasa biyayyar nan ba?

19 Sai muka ga, ashe, saboda rashin bangaskiyarsu ne suka kāsa shiga.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan