Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ibraniyawa 2 - Littafi Mai Tsarki


Maganar Ceto Mai Girma

1 Saboda haka, lalle ne mu ƙara mai da hankali musamman ga abubuwan da muka ji, don kada mu yi sakaci, su sulluɓe mana.

2 In kuwa maganar nan da aka faɗa ta bakin mala'iku ta zama tabbatacciya, har kowane keta umarni da rashin biyayya, suka gamu da sakamakonsu wanda ya kamace su,

3 to, ta ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi kula da ceto mai girma haka? Domin Ubangiji kansa, shi ne ya fara sanar da shi, waɗanda suka saurare shi kuma suka tabbatar mana da shi,

4 sa'an nan kuma Allah ya haɗa shaidarsa, da tasu a kan ceton, ta alamu da abubuwan al'ajabi da mu'ujizai iri iri, da kuma baiwar Ruhu Mai Tsarki dabam dabam da ya rarraba kamar yadda ya nufa.


Shugaban Ceto

5 Ai, ba ga mala'iku ba ne Allah ya sa mulkin duniyar da za a yi, wanda muke zance.

6 Amma wani ya tabbatar a wani wuri cewa, “Mutum ma mene ne, har da za ka tuna da shi? Ko ɗan mutum ma, har da za ka kula da shi?

7 Kā sa shi ya gaza mala'iku a ɗan lokaci kaɗan, Kā naɗa shi da ɗaukaka da girma, Kā ɗora shi a kan dukkan halittarka.

8 Kā sarayar da kome a ƙarƙashin ikonsa.” To, a wajen sarayar da dukkan abubuwa a ƙarƙashinsa ɗin nan, Allah bai bar kome a keɓe ba. Amma kuwa har a yanzu ba mu ga yana sarrafa dukkan abubuwa ba.

9 Amma muna ganin Yesu, wanda a ɗan lokaci aka sa shi ya gaza mala'iku, an naɗa shi da ɗaukaka da girma, saboda shan wuyarsa ta mutuwa. Wannan kuwa duk ta wurin alherin Allah ne Yesu ya mutu saboda kowa.

10 Saboda haka, ya dace da Allah, shi da dukkan abubuwa suka kasance dominsa, ta gare shi ne kuma dukkan abubuwa suka samu, yă kammala shugaban cetonsu ta wurin shan wuya, a wajen kawo 'ya'ya masu yawa ga samun ɗaukaka.

11 Domin da shi mai tsarkakewar da kuma waɗanda aka tsarkaken, duk tushensu ɗaya ne. Shi ya sa ba ya jin kunyar kiransu 'yan'uwansa,

12 da ya ce, “Zan sanar da sunanka ga 'yan'uwana, A tsakiyar ikilisiya zan yabe ka da waƙa.”

13 Har wa yau, ya ce, “Zan dogara a gare shi.” Da kuma, “Ga ni nan, ni da 'ya'yan da Allah ya ba ni.”

14 Wato tun da yake 'ya'yan duk suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamannin haka, domin ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato iblis, ta wurin mutuwarsa,

15 yă kuma 'yanta duk waɗanda tun haihuwarsu suke zaman bauta saboda tsoron mutuwa.

16 Don hakika ba mala'iku yake taimako ba, a'a, zuriyar Ibrahim ne yake taimako.

17 Saboda haka, lalle ne yă zama kamar 'yan'uwansa ta kowane hali, domin yă zama Babban Firist, mai jinƙai, mai aminci kuma na al'amarin Allah, yă kuma miƙa hadayar sulhu ta gafarta zunuban jama'a.

18 Tun da yake shi ma ya sha wuya, sa'ad da aka gwada shi, ashe, zai taimaki waɗanda ake yi wa gwaji.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan