Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ibraniyawa 13 - Littafi Mai Tsarki


Gudunmawar da yake Faranta wa Allah Rai

1 Sai ku nace da ƙaunar 'yan'uwa.

2 Kada ku daina yi wa baƙi alheri, gama ta haka ne waɗansu suka sauki mala'iku ba da sani ba.

3 Ku riƙa tunawa da waɗanda suke kurkuku, kamar tare kuke a ɗaure, da kuma waɗanda ake gwada wa wuya, kamar ku ake yi wa.

4 Kowa yă girmama aure, Gădon aure kuwa yă zauna marar dauɗa, don fasikai da mazinata Allah zai hukunta su,

5 Kada halinku ya zama na son kuɗi. Ku dangana da abin da kuke da shi, gama Allah kansa ya ce, “Har abada ba zan bar ka ba. Har abada kuma ba zan yashe ka ba.”

6 Saboda haka, ma iya fitowa gabagaɗi, mu ce, “Ubangiji shi ne mataimakina, Ba zan ji tsoro ba. Me mutum zai iya yi mini?”

7 Ku tuna da shugabanninku na dā, waɗanda suka faɗa muku Maganar Allah. Ku dubi ƙarshensu, ku kuma yi koyi da bangaskiyarsu.

8 Yesu Almasihu ba ya sākewa, shi ne a jiya, da yau, hakika har abada ma.

9 Kada baƙuwar koyarwa iri iri ta bauɗar da ku, ai, abu ne mai kyau alherin Allah ya zamana shi yake ƙarfafa zuciya, ba abinci iri iri ba, waɗanda ba su amfani ga masu dogara da su.

10 Muna da bagadin hadaya, wanda masu ibada a alfarwar nan ba su da izini su ci abincin wurin,

11 domin naman dabbobin da babban firist yake ɗiban jininsu yă kai Wuri Mafi Tsarki domin kawar da zunubai, akan ƙone shi ne a bayan zango.

12 Haka ma, Yesu ya sha wuya a waje bayan birni, domin yă tsarkake jama'a da nasa jini.

13 Saboda haka, sai mu fita mu je a gare shi a bayan zango, muna shan irin wulakancin da aka yi masa.

14 Domin ba mu da wani dawwamammen birni a nan, birnin nan mai zuwa muke nema.

15 To, a koyaushe, sai mu yi ta yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa.

16 Kada kuwa ku daina yin alheri da gudunmawa, domin irin waɗannan su ne suke faranta wa Allah rai.

17 Ku yi wa shugabanninku biyayya, ku bi umarnansu, don su ne masu kula da rayukanku, su ne kuma za su yi lissafin aikinsu, don su yi haka da farin ciki, ba da baƙin ciki ba, don in sun yi da baƙin ciki ba zai amfane ku ba.

18 Ku yi mana addu'a, gama mun tabbata muna da lamiri mai kyau, muna kuwa so mu tafiyar da al'amuranmu da halin kirki ne.

19 Musamman nake tsananta roƙonku ku yi haka, don a hanzarta a komo da ni a gare ku.


Sa Albarka da kuma Gaisuwa

20 Allah mai zartar da salama, wanda ya ta da Ubangijinmu Yesu, Makiyayin tumaki mai girma, daga matattu, albarkacin jinin nan na tabbatar madawwamin alkawari,

21 yă kamala ku da kowane irin kyakkyawan abu, domin ku aikata nufinsa, yă kuma aikata a cikinmu abin da yake faranta masa rai ta wurin Yesu Almasihu. Ɗaukaka tā tabbata a gare shi har abada abadin. Amin, Amin.

22 To, ina roƙonku, 'yan'uwa, ku yi haƙuri da gargaɗina, don taƙaice na rubuto muku.

23 Ku sani, an sāki ɗanuwanmu Timoti, da shi ma za mu gan ku, in ya zo da wuri.

24 Ku gai da dukan shugabanninku, da kuma dukan tsarkaka. Waɗanda suke daga ƙasar Italiya suna gaishe ku.

25 Alharin Ubangiji yă tabbata a gare ku, ku duka. Amin.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan