Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ibraniyawa 12 - Littafi Mai Tsarki


Horon Ubangiji

1 Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri,

2 muna zuba ido ga Yesu, shi da yake shugaban bangaskiyarmu, da kuma mai kammala ta, wanda domin farin cikin da aka sa a gabansa ya daure wa gicciye, bai mai da shi wani abin kunya ba, a yanzu kuma a zaune yake a dama ga kursiyin Allah.

3 Ku fa, dubi wannan da ya jure irin gābar nan da masu zunubi suka sha yi da shi, don kada ku gaji, ko kuwa ku karai.

4 Famarku da zunubi ba ta kai har yadda za a kashe ku ba.

5 Kun kuma mance da gargaɗin nan da Allah ya yi muku a kan ku 'ya'yansa ne, wato “Ya ɗana, kada ka raina horon Ubangiji, Kada kuma ka karai, in ya kwaɓe ka.

6 Domin Ubangiji, wanda yake ƙauna, shi yake horo, Yakan kuma hori duk ɗan da ya karɓa.”

7 Shan wuyar da kuke jurewa, ai, duk don horo ne. Allah ya riƙe ku, ku 'ya'yansa ne. To, wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa?

8 In kuwa ba ku da horo irin horon da ake yi wa kowa, to, ashe, kun zama shegu ke nan, ba 'yan halal ba.

9 Har wa yau kuma, ai, muna da ubanninmu na jiki da suke hore mu, mun kuwa yi musu ladabi. Ashe, ba za mu fi yi wa Uban ruhohinmu biyayya ƙwarai ba, mu rayu?

10 Su kam, sun hore mu a ɗan lokaci kaɗan don ganin damarsu, amma shi, don amfanin kanmu ne yake horonmu, domin mu zama abokan tarayya a cikin tsarkinsa.

11 Ai, kowane irin horo, a lokacin shansa, abu ne mai baƙin ciki, ba na farin ciki ba. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.


Faɗakarwa a kan Ƙin Alherin Allah

12 Domin wannan, ku miƙe hannuwanku da suke reto, da gwiwoyinku marasa ƙarfi.

13 Ku bi miƙaƙƙun hanyoyi ɗoɗar, don kada mai ɗingishi ya gulle, a maimakon ya warke.

14 Ku himmantu ga zaman lafiya da kowa, ku kuma zama a tsarkake, in banda shi kuwa, ba wanda zai ga Ubangiji.

15 Ku kula fa, kada kowa yă kāsa samun alherin Allah, kada kuma wani tushen ɗacin rai ya tabbata, ya haddasa ɓarna, har ya ɓata mutane masu yawa ta haka,

16 kada kuma wani yă zama fasiki, ko mai sāɓon Allah, kamar isuwa, wanda ya sayar da hakkinsa na ɗan fari a kan cimaka a ɗaya tak.

17 Kun dai sani daga baya, da ya so yă gāji albarkar nan, sai aka ƙi shi, domin bai sami hanyar tuba ba, ko da yake ya yi ta nemanta har da hawaye.

18 Ai, ba ga abin da za a taɓa ne, kuka iso ba, ko wuta mai ruruwa, ko baƙin duhu duhu ƙirin, ko hadiri,

19 ko ƙarar ƙaho, ko wata murya, wadda har masu jin maganarta suka yi roƙo kada su ƙara ji,

20 don ba su iya jure umarnin da aka yi musu ba cewa, “Ko da dabba ce ta taɓa dutsen, sai a kashe ta da jifa.”

21 Amma ganin wannan abu da matuƙar bantsoro yake! Har ma Musa ya ce, “Ina rawar jiki don matuƙar tsoro.”

22 Amma ku kun iso Ɗutsen Sihiyona ne, da birnin Allah Rayayye, Urushalima ta Sama, wurin dubban mala'iku.

23 Kun iso taron farin ciki na kirayayyun 'ya'yan fari na Allah, waɗanda sunayensu suke a rubuce a Sama. Kun iso wurin Allah, wanda yake shi ne mai yi wa kowa shari'a, da kuma wurin ruhohin mutane masu adalci, waɗanda aka kammala.

24 Kun iso wurin Yesu, matsakancin sabon alkawari, da kuma wurin jinin nan na tsarkakewa, wanda yake yin mafificiyar magana fiye da na Habila.

25 Ku kula fa, kada ku ƙi mai maganar nan. Domin in waɗanda suka ƙi jin mai yi musu gargaɗi a duniya ba su tsira ba, to, ƙaƙa mu za mu tsira, in mun ƙi jin wannan da yake yi mana gargaɗi ma daga Sama?

26 A lokacin nan muryarsa ta girgiza duniya, amma a yanzu ya yi alkawari cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak, ba duniya kaɗai zan girgiza ba, amma har sama ma.”

27 To, wannan cewa, “Har wa yau dai sau ɗaya tak,” ya nuna kawar da abubuwan da aka girgiza, wato abubuwan da aka halitta, don abubuwan da ba sa girgizuwa su wanzu.

28 Saboda haka, sai mu yi godiya domin mun sami mulkin da ba ya girgizuwa, ta haka kuma mu yi wa Allah sujada abar karɓa, tare da tsoro da tsananin girmamawa,

29 domin Allahnmu wuta ne mai cinyewa.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan