Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ibraniyawa 10 - Littafi Mai Tsarki

1 To, tun da yake Shari'a ishara ce kawai ta kyawawan abubuwan da suke a gaba, ba ainihin siffarsu ba, ashe, har abada ba za ta iya kammala waɗanda suke kusatar Allah ta wurin waɗannan hadayu ba, waɗanda ake yi a kai a kai kowace shekara.

2 In haka ne kuwa, ashe, ba sai a daina yin hadayar ba? Da an taɓa tsarkake masu ibadar nan sarai, ai, da ba su ƙara damuwa da zunubai ba.

3 Amma a game da irin waɗannan hadayu, akan tuna da zunubai a kowace shekara,

4 domin ba mai yiwuwa ba ne jinin bijimai da na awaki ya ɗauke zunubi.

5 Shi ya sa da Almasihu zai shigo duniya, sai ya ce, “Hadaya da sadaka kam, ba ka so, Amma kā tanadar mini jiki.

6 Ba ka farin ciki da hadayar ƙonewa, da kuma hadayar kawar da zunnbai.

7 Sa'an nan na ce, ‘Ga ni, na zo in aikata nufinka, ya Allah,’ Kamar yadda yake a rubuce a game da ni a Littafi.”

8 Sa'ad da ɗazu ya ce, “Ba ka son hadaya, da sadaka, da hadayar ƙonewa, da hadayar kawar da zunubai, ba ka kuwa jin daɗinsu,” wato, irin waɗanda ake miƙawa ta hanyar Shari'a,

9 sai kuma ya ƙara da cewa, “Ga ni, na zo in aikata nufinka.” Ya kawar da na farkon ne, don yă kafa na biyun.

10 Ta nufin nan ne aka tsarkake mu, ta wurin miƙa jikin Yesu Almasihu hadaya sau ɗaya tak, ba ƙari.

11 Har wa yau kuma, kowane firist yakan tsaya a kan hidimarsa kowace rana, yana miƙa hadaya iri ɗaya a kai a kai, waɗanda har abada ba za su iya ɗauke zunubai ba.

12 Amma shi Almasihu da ya miƙa hadaya guda ta har abada domin kawar da zunubai, sai ya zauna a dama ga Allah,

13 tun daga lokacin nan yana jira, sai an sa ya take maƙiyansa.

14 Gama ta hadaya guda kawai ya kammala waɗanda aka tsarkake har abada.

15 Ruhu Mai Tsarki ma yana yi mana shaida haka, domin bayan ya ce,

16 “Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu,”

17 sai kuma ya ƙara cewa, “Ba kuma zan ƙara tunawa da zunubansu da laifofinsu ba.”

18 To, a inda aka sami gafarar waɗannan, ba sauran wata hadaya domin kawar da zunubi.


Mu Matsa Kusa, Mu Dage

19 Saboda haka, ya 'yan'uwa, tun da muke da amincewar shiga Wuri Mafi Tsarki, ta wurin jinin Yesu,

20 ta wurin sabuwar hanya, rayayyiya wadda ya buɗe mana ta labulen nan, wato jikinsa,

21 da yake kuma muna da Firist mai girma, mai mulkin jama'ar Allah,

22 sai mu matsa kusa, da zuciya ɗaya, da cikakkiyar bangaskiya tabbatacciya, da zukatunmu tsarkakakku daga mugun lamiri, jikinmu kuma wankakke da tsattsarkan ruwa.

23 Sai mu tsaya da ƙarfi a kan bayyana yarda ga begen nan namu, domin shi mai yin alkawarin nan amintacce ne,

24 mu kuma riƙa kula da juna, ta yarda za mu ta da juna a tsimi mu mu yi ƙauna da aika nagari.

25 Kada mu bar yin taronmu, yadda waɗansu suke yi, sai dai mu ƙarfafa wa juna zuciya, tun ba ma da kuka ga ranar nan tana kusatowa ba.

26 In kuwa mun ci gaba da yin zunubi da gangan, bayan mun yi na'am da sanin gaskiya, to, ba fa sauran wata hadaya domin kawar da zunubai,

27 sai dai matsananciyar fargabar hukunci, da kuma wuta mai tsananin zafi, wadda za ta cinye maƙiyan Allah.

28 Kowa ya yar da Shari'ar Musa, akan kashe shi ba tausayi, a kan shaidu biyu ko uku.

29 To mutumin da ya raina Ɗan Allah, ya kuma tozarta jinin nan na tabbatar alkawari, wanda aka tsarkake shi da shi, har ya wulakanta Ruhun alheri, wane irin hukunci mafi tsanani kuke tsammani ya cancanta fiye da wancan?

30 Domin mun san shi, shi wanda ya ce, “Ramuwa tawa ce, ni zan sāka.” Da kuma, “Ubangiji zai yi wa jama'arsa hukunci.”

31 Abu ne fa mai matuƙar bantsoro a fāɗa a cikin hukuncin Allah Rayayye.

32 Amma dai ku tuna, a shekarun baya, bayan da aka haskaka zukatanku, kun jure tsananin fama da shan wuya,

33 wata rana ana zaginku, ana ta wahalshe ku, ana wulakanta ku a gaban jama'a, wata rana kuma kuna mai da kanku ɗaya da waɗanda aka yi wa haka,

34 domin kun ji tausayin ɗaurarru, kun kuma yarda da daɗin rai da wason da aka yi muku, tun da yake kun sakankance kuna da mallaka mafi kyau, mai tabbata kuwa.

35 Saboda haka, kada ku yar da amincewar nan taku, domin tana da sakamako mai yawa.

36 Gama yin jimiri ya kama ku, domin bayan da kun aikata nufin Allah, ku sami abin da aka yi muku alkawari.

37 “Sauran lokaci kaɗan, Mai zuwan nan zai zo, ba kuwa zai yi jinkiri ba.

38 Amma adalina, ta wurin bangaskiya zai rayu. Amma in ya ja da baya, ba zan yi farin ciki da shi ba.”

39 Amma mu ba a cikin waɗanda suke ja da baya su hallaka muke ba, mu a cikin masu bangaskiya muke, mai kai mu ga ceton rayukanmu.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan