Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Ibraniyawa 1 - Littafi Mai Tsarki


Allah Ya Yi Magana ta wurin Ɗansa

1 A zamanin dā, Allah ya yi wa kakannin kakanninmu magana ta hanyoyi masu yawa iri iri, ta bakin annabawa,

2 amma a zamanin nan na ƙarshe, sai ya yi mana magana ta wurin Ɗansa, wanda ya sa magājin kome, wanda ta wurinsa ne kuma ya halicci duniya.

3 Shi ne hasken ɗaukakar Allah, ainihin kamannin zatinsa kuma, shi kuma yana a riƙe da dukan abubuwa ta ikon faɗarsa. Bayan da ya tsarkake zunubanmu, sai ya zauna a dama da Maɗaukaki a can Sama.


Fifikon Yesu a kan Mala'iku

4 Ta haka yake da fifiko a kan mala'iku, kamar yadda sunansa da ya gāda yake da fifiko nesa a kan nasu.

5 Domin kuwa wane ne a cikin mala'iku Allah ya taɓa ce wa, “Kai Ɗana ne, Ni Ubanka ne yau”? da kuma, “Zan kasance Uba a gare shi, Shi kuma, zai kasance Ɗa a gare ni”?

6 Amma da zai sāke shigo da magāji a duniya, sai ya ce, “Dukkan mala'ikun Allah su yi masa sujada.”

7 A game da mala'iku kuma sai ya ce, “Yakan mai da mala'ikunsa ruhohi, Masu hidimarsa kuma harsunan wuta.”

8 Amma a game da ɗan, sai ya ce, “Kursiyinka, ya Allah, na har abada abadin ne, Sandar sarautarka sanda ce ta tsantsar gaskiya.

9 Kā ƙaunaci aikin adalci, kā ƙi aikin sāɓo. Saboda haka Allah, wato, Allahnka, ya shafe ka Da man farin ciki fiye da tsararrakinka.”

10 Da kuma, “Ya ubangiji, kai ne ka halicci duniya tun farko, Sammai kuma aikinka ne.

11 Su za su hallaka, amma kai madawwami ne. Duk za su tsufa kamar tufa,

12 Za ka naɗe su kamar mayafi, Za su kuma sauya, Amma kai kana nan ba sākewa, Har abada shekarunka ba za su ƙare ba.”

13 Amma wane ne a cikin mala'iku Allah ya taɓa ce wa, “Zauna a damana, Sai na sa ka take maƙiyanka”?

14 Ashe, dukan mala'iku ba ruhohi masu hidima ba ne, waɗanda Allah yakan aika, don su yi wa waɗanda za su gāji ceto hidima?

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan