Ezra 2 - Littafi Mai TsarkiYawan Kamammu da suka Komo. ( Neh 7.4-73 ) 1 Waɗannan su ne mutanen da suka bar lardin Babila suka komo Urushalima da Yahuza daga bautar talala da Nebukadnezzar, Sarkin Babila, ya kai su Babila. Kowa ya koma garinsu. 2 Sun komo tare da Zarubabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Seriya, da Re'elaya, da Mordekai, da Bilshan, Misfar, da Bigwai, da Rehun, da Ba'ana. Ga jerin iyalan Isra'ila, da yawan waɗanda suka komo na kowane iyali daga zaman talala. 3-20 Zuriyar Farosh, mutum dubu biyu da ɗari da saba'in da biyu (2,172) Zuriyar Shefatiya, mutum ɗari uku da saba'in da biyu Zuriyar Ara, mutum ɗari bakwai da saba'in da biyar Zuriyar Fahat-mowab na zuriyar Yeshuwa da Yowab, mutum dubu biyu da ɗari takwas da goma sha biyu (2,812) Zuriyar Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) Zuriyar Zattu, mutum ɗari tara da arba'in da biyar Zuriyar Zakkai, mutum ɗari bakwai da sittin Zuriyar Bani, mutum ɗari shida da arba'in da biyu Zuriyar Bebai, mutum ɗari shida da ashirin da uku Zuriyar Azgad, mutum dubu da ɗari biyu da ashirin da biyu (1,222) Zuriyar Adonikam, mutum ɗari shida da sittin da shida Zuriyar Bigwai, mutum dubu biyu da hamsin da shida (2,056) Zuriyar Adin, mutum ɗari huɗu da hamsin da huɗu Zuriyar Ater na Hezekiya, mutum tasa'in da takwas Zuriyar Bezai, mutum ɗari uku da ashirin da uku Zuriyar Yora, mutum ɗari da goma sha biyu Zuriyar Hashum, mutum ɗari biyu da ashirin da uku Zuriyar Gibeyon, mutum tasa'in da biyar. 21-35 Mutanen da suke a garuruwan nan, su ma suka komo. Mutanen Baitalami, mutum ɗari da ashirin da uku Mutanen Netofa, mutum hamsin da shida Mutanen Anatot, mutum ɗari da ashirin da takwas Zuriyar Azmawet, mutum arba'in da biyu Zuriyar Kiriyat-yeyarim, da Kefira, da Biyerot, mutum ɗari bakwai da arba'in da uku Zuriyar Rama da Geba, mutum ɗari shida da ashirin da ɗaya Mutanen Mikmash, mutum ɗari da ashirin da biyu Mutanen Betel da Ai, mutum ɗari biyu da ashirin da uku Zuriyar Nebo, mutum hamsin da biyu Zuriyar Magbish, mutum ɗari da hamsin da shida Zuriyar wancan Elam, mutum dubu da ɗari biyu da hamsin da huɗu (1,254) Zuriyar Harim, mutum ɗari uku da ashirin Zuriyar Lod, da Hadid, da Ono, mutum ɗari bakwai da ashirin da biyar Mutanen Yariko, mutum ɗari uku da arba'in da biyar Zuriyar Senaya, mutum dubu uku da ɗari shida da talatin (3,630). 36-39 Ga kuma lissafin iyalan firistocin da suka komo, Zuriyar Yedaiya na gidan Yeshuwa, mutum ɗari da saba'in da uku Zuriyar Immer, mutum dubu da hamsin da biyu (1,052) Zuriyar Fashur, mutum dubu da ɗari biyu da arba'in da bakwai (1,247). Zuriyar Harim, mutum dubu da goma sha bakwai (1,017). 40 Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel na Hodawiya mutum saba'in da huɗu. 41 Mawaƙa na zuriyar Asaf, mutum ɗari da ashirin da takwas. 42 Zuriyar Shallum, da ta Ater, da ta Talmon, da ta Akkub, da ta Hatita, da ta Shobai, su ne zuriyar matsaran ƙofa, yawan mutanensu duka ɗari da talatin da tara. 43-54 Ga lissafin ma'aikatan Haikali da suka komo. Zuriyar Ziha, da zuriyar Hasufa, da zuriyar Tabbawot Zuriyar Keros, da zuriyar Siyaha, da zuriyar Fadon Zuriyar Lebana, da zuriyar Hagaba, da zuriyar Akkub Zuriyar Hagab, da zuriyar Shamlai, da zuriyar Hanan Zuriyar Giddel, da zuriyar Gahar, da zuriyar Rewaiya Zuriyar Rezin, da zuriyar Nekoda, da zuriyar Gazam Zuriyar Ussa, da zuriyar Faseya, da zuriyar Besai Zuriyar Asna, da Me'uniyawa, da Nefushiyawa Zuriyar Bakbuk, da zuriyar Hakufa da zuriyar Harhur Zuriyar Bazlut, da zuriyar Mehida, da zuriyar Harsha Zuriyar Barkos, da zuriyar Sisera, da zuriyar Tema Zuriyar Neziya, da zuriyar Hatifa. 55-57 Zuriyar barorin Sulemanu, su ne Zuriyar Sotai, da zuriyar Hassoferet, da zuriyar Feruda Zuriyar Yawala, da zuriyar Darkon, da zuriyar Giddel Zuriyar Shefatiya, da zuriyar Hattil, da zuriyar Fokeret-hazzebayim, da zuriyar Ami. 58 Dukan zuriyar ma'aikatan Haikali da zuriyar barorin Sulemanu su ɗari uku da tasa'in da biyu ne. 59 Waɗannan su ne waɗanda suka zo daga Tel-mela, da Tel-harsha, da Kerub, da Addan, da Immer, amma ba su iya tabbatar da gidajen kakanninsu da asalinsu ba, ko su na Isra'ila ne. 60 Su ne zuriyar Delaiya, da zuriyar Tobiya, da zuriyar Nekoda. Su ɗari shida da hamsin da biyu ne. 61 Sai kuma zuriyar firistoci, wato zuriyar Habaya, da zuriyar Hakkoz, da zuriyar Barzillai, wanda ya auri mata daga cikin 'ya'yan Barzillai, mata, mutumin Gileyad, aka kira shi da sunnansu, 62 suka bincika littafin asalin kakanninsu, amma suka ga ba su a ciki. Don haka aka mai da su ƙazantattu, ba a yarda musu su yi aikin firist ba. 63 Sai mai mulki ya ce ba za su ci abinci mafi tsarki ba, sai firist ya shawarci Urim da Tummim tukuna, wato kamar kuri'a ke nan. 64-67 Yawan taron jama'a su dubu arba'in da biyu da ɗari uku da sittin (42,360). Barorinsu maza da mata, dubu bakwai da ɗari uku da talatin da bakwai (7,337) Mawaƙa ɗari biyu mata da maza Dawakansu ɗari bakwai da talatin da shida Alfadaransu ɗari biyu da arba'in da biyar Raƙumansu kuma ɗari huɗu da talatin da biyar ne Jakunansu kuwa dubu shida da ɗari bakwai da ashirin (6,720). 68 Waɗansu shugabannin gidajen kakanninsu, sa'ad da suka isa Haikalin Ubangiji a Urushalima, sai suka bayar da kyautai da yardar rai don a sāke gina Haikalin Ubangiji a wurin da yake dā. 69 Gwargwadon arzikinsu suka ba da darik dubu sittin da dubu ɗaya (61,000) na zinariya, da maina dubu biyar (5,000) na azurfa, da tufafin firistoci guda ɗari. 70 Firistoci, da Lawiyawa, da waɗansu mutanen da suke zaune a Urushalima da kewayenta, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da ma'aikatan Haikalin, da dukan mutanen Isra'ila suka zauna a garuruwansu. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria