Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Esta 10 - Littafi Mai Tsarki


Ƙasaitar Mordekai

1 Sarki Ahasurus ya fasa haraji a ƙasar tudu da ta bakin teku.

2 An rubuta a littafin tarihin sarakunan Mediya da na Farisa, dukan ayyukan iko, da isa, da cikakken labarin darajar Mordekai, wadda sarki ya ba shi.

3 Gama sarki Ahasurus kaɗai yake gaba da Mordekai Bayahude, Mordekai kuma yana da girma a wurin Yahudawa, yana kuma da farin jini a wurin taron jama'ar 'yan'uwansa, gama ya nemi lafiyar jama'arsa, yana kuma maganar alheri ga dukan mutane.

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan