Ayuba 25 - Littafi Mai TsarkiBildad Bai Yarda Allah Zai Baratar da Mutum Ba 1 Bildad ya amsa. 2 “Allah mai iko ne, duka sai a ji tsoronsa, A samaniya yake tafiya da mulkinsa da salama. 3 Akwai wanda zai iya ƙidaya mala'ikun da suke masa hidima? Akwai wurin da hasken Allah bai haskaka ba? 4 Akwai wanda ya isa ya zama adali, Ko mai tsarki a gaban Allah? 5 Hasken wata ba haske ba ne a gare shi, Ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa. 6 To, mutum fa? Ai, wannan tsutsa ne, ɗan ƙwaro kawai. Me mutum ya daɗa a gaban Allah?” |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria