Amos 9 - Littafi Mai TsarkiBa a Kauce wa Hukuncin Allah 1 Na ga Ubangiji na tsaye a wajen bagade. Ya yi umarni, ya ce, “Bugi ginshiƙan Haikali don shirayi duka yă girgiza. Farfasa su, su fāɗi a kan mutane! Sauran mutane kuwa, Zan kashe su a wurin yaƙi. Ba wanda zai tsere, ko ɗaya. 2 Ko da za su nutsa zuwa lahira, Zan kama su. Ko sun hau Sama, Zan turo su. 3 Ko da za su hau su ɓuya a bisa ƙwanƙolin Dutsen Karmel, Zan neme su in cafko su. Ko da za su ɓuya mini a ƙarƙashin teku, Sai in sa dodon ruwa yă yayyage su. 4 Idan kuwa abokan gābansu ne suka kama su, In umarce su su hallaka su da takobi, Tun da na yi ƙudurin ƙare su.” 5 Ubangiji Allah Mai Runduna Ya taɓi duniya, ta girgiza. Duk waɗanda suke zaune cikinta Suna baƙin ciki. Duniya duka takan hau Ta kuma gangara kamar ruwan Kogin Nilu. 6 Ubangiji ya gina al'arshinsa a sama, Ya shimfiɗa samaniya a bisa duniya. Ya sa ruwan teku ya zo, Ya kwarara shi a bisa duniya. Sunansa Ubangiji ne! 7 Ubangiji ya ce, “Jama'ar Isra'ila, Ina yi da ku daidai yadda nake yi da Habashawa. Na fito da Filistiyawa daga Kaftor, Suriyawa kuwa daga Kir, Daidai yadda na fito da ku daga Masar. 8 Ina dai kallon mulkin nan mai zunubi. Zan hallaka su daga duniya, Amma ba zan hallaka dukan jama'ar Yakubu ba. 9 “Zan umarta a rairayi jama'ar Isra'ila Da matankaɗi kamar hatsi. Zan rairaye su daga cikin sauran al'umma, Duk da haka ko ƙwaya ɗaya ba za ta salwanta ba. 10 Masu zunubi daga cikin jama'ata za su mutu a yaƙi, Wato dukansu da suke cewa, ‘Allah ba zai bar wata masifa ta kusace mu ba!’ ” Ceton da Za a Yi wa Isra'ila Nan Gaba 11 “Wata rana zan sāke tayar da birnin Dawuda Tankar yadda akan ta da gidan da ya rushe. Zan gyara garunsa, in sāke mai da shi. Zan sāke gina shi in mai da shi kamar yadda yake tun dā. 12 Ta haka jama'ar Isra'ila za ta ci nasara bisa sauran ƙasar Edom wadda ta ragu, Da bisa dukan al'umman da a dā su nawa ne,” In ji Ubangiji, wanda zai sa al'amarin ya auku. 13 Ubangiji ya ce, “Kwanaki suna zuwa, Sa'ad da girbi zai bi bayan huda nan da nan, Matsewar ruwan inabi kuma Za ta bi bayan shuka nan da nan. Duwatsu za su zubo da ruwan inabi mai zaƙi, Tuddai kuma su gudano da shi. 14 Zan komo da mutanena ƙasarsu, Za su giggina biranensu da suka rurrushe, Su zauna a cikinsu. Za su shuka gonakin inabi, su sha ruwan inabin. Za su yi lambuna, su ci amfaninsu. 15 Zan dasa su a ƙasar da na ba su, Ba kuwa za a ƙara tumɓuke su ba.” Ubangiji Allahnku ne ya faɗa. |
@Bible Society of Nigeria 1979
Bible Society of Nigeria