Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -

Amos 8 - Littafi Mai Tsarki


Wahayi na Huɗu, Kwandon Ɓaure na Ci

1 Ubangiji ya nuna mini wahayi, sai na ga kwandon ɓaure na ci.

2 Sai Ubangiji ya ce, “Amos, me ka gani?” Na ce, “Kwandon ɓaure na ci.” Ubangiji kuma ya ce mini, “Ƙarshen jama'ata Isra'ila ya zo. Ba zan sāke nufina a kan yi musu hukunci ba.

3 Waƙoƙin da akan raira a fāda, za su zama na makoki a wannan rana. Za a iske gawawwaki ko'ina. Ba za a ji motsin kome ba.”


An kai Ƙarshen Isra'ila

4 Ku ji wannan, ku da kuke tattake masu bukata, kuna ƙoƙari ku hallakar da matalautan ƙasar.

5 Kuna ce wa kanku, “Mun ƙosa keɓaɓɓun kwanakin nan su wuce, Mu sami damar yin kasuwancinmu. Yaushe Asabar ɗin za ta ƙare ne? Ko mā sami damar kai hatsinmu kasuwa, Mu sayar musu da tsada, Mu yi awo da ma'aunin zalunci, Mu daidaita ma'auni yadda za mu cuci mai saya?

6 Za mu sayi matalauci da azurfa ya zama bawa, Mai fatara kuma da takalma bi-shanu. Za mu sayar da ruɓaɓɓen hatsi, Mu ci riba mai yawa.”

7 Ubangiji Allahn Isra'ila ya riga ya rantse, Ya ce, “Ba zan manta da mugayen ayyukanku ba.

8 Shi ya sa ƙasar za ta girgiza, Duk wanda yake cikinta zai yi baƙin ciki. Ƙasa duka za ta girgiza. Za ta hau ta sauka kamar Kogin Nilu.

9 A wannan lokaci rana za ta fāɗi da tsakar rana, Duniya ta duhunta da rana kata. Ni, Ubangiji ne na faɗa.

10 Zan mai da bukukuwanku makoki, In sa waƙoƙinku na murna su zama na makoki. Zan sa muku tufafin makoki, In sa ku aske kanku. Za ku yi makoki kamar iyayen da suka rasa tilon ɗansu. Ranan nan mai ɗaci ce har ƙarshe.

11 “Lokaci yana zuwa da zan aiko da yunwa a ƙasar. Mutane za su ji yunwa, Ba ta abinci ba, Za su ji ƙishi, Ba na ruwa ba. Za su ji yunwar rashin samun saƙo daga wurin Ubangiji. Ni Ubangiji ne, na faɗa.

12 Mutane za su raunana, su riƙa kai da kawowa, Daga gabas zuwa yamma, daga kuma kudu zuwa arewa. Za su dudduba ko'ina suna neman saƙo daga Ubangiji, Ba kuwa za su samu ba.

13 A ranan nan kyawawan 'yan mata da samari Za su faɗi saboda ƙishirwa.

14 Waɗanda suka yi rantsuwa da gumakan Samariya, Waɗanda suka ce, ‘Na rantse da gunkin Dan, Da ran gunkin Biyer-sheba,’ Irin waɗannan mutane za su fāɗi, Ba za su ƙara tashi ba.”

@Bible Society of Nigeria 1979

Bible Society of Nigeria
Lean sinn:



Sanasan